Ganduje ya yi magana kan daliban Islamiyya 20 da suka mutu a hatsarin jirgin ruwa a Kano
- Gwamnan jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya bayyana rashin jin daɗinsa bisa hatsarin jirgin ruwa da ya faru a Kano
- Ganduje ya roki matukan jirgin ruwa su daina cika wa abun hawan su kaya har ya fi ƙarfinsa, domin rayuwar mutane ce a gaba
- Ya kuma yi addu'ar samun rahamar ubangiji ga waɗan da suka mutu, tare da fatan samun lafiya ga waɗan da ke kwance a Asibiti
Kano - Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na jihar Kano, ya nuna damuwarsa kan hatsarin jirgin ruwa a Bagwai, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutum 20.
Ganduje ya yi magana ne ta bakin sakataren watsa labaransa, Abba Anwar, a wata sanarwa da ya fitar ranar Laraba a Kano.
The Nation ta rahoto wani sashin sanarwan yace:
"Hatsarin kwalekwale a Bagwai wanda ya yi sanadin mutuwar mutum 20, yayin da ake cigaba da aikin ceto, ya girgiza jihar Kano baki ɗaya."
"Mun samu labarin cewa kwalekwalen ya taso ne daga Kauyen Hayin Badau, a kan hanyarsu ta zuwa wurin taron Maulidi."
"Kwalekwalen na ɗauke da mutum 50 da sauran wasu kayayyaki da aka jibga masa, kuma ana zargin ya kife ne saboda nauyi ya masa yawa. Mafi yawan fasinjojin daliban Islamiyya ne."
Ganduje ya yi ta'aziyya da fatan rahama
Gwamna Ganduje ya yi addu'an Allah ya gafarta wa mamatan kurakuransu, waɗan da suka tsira kuma Allah ya basu lafiya cikin sauri.
"Ina rokon masu jirgin ruwa su daina cika wa abun hawan su kaya, zasu samu riba ko ba su yi haka ba."
"Ya kamata mutane su san cewa rayuwar yan uwansu mutane tana da matukar daraja kuma ta wuce a jefa su cikin hatsari."
"Daga bayanan da muka samu yau da safe mutum 20 sun mutu, kuma an kwantar da wasu mutum 7 a Asibiti da kuma wasu 8 da aka gano yau da safe. Har yanzun ana cigaba da nemo sauran."
A wani labarin na daban kuma An tsinci gawar wani mutumi mai aure, da wata Amarya a cikin mota a Kano
Rahotanni daga jihar Kano sun bayyana cewa an tsinci gawar wasu mutum biyu, mace da namiji a cikin mota.
Hukumar yan sanda tace namijin yana da mata har da ƴaƴa, yayin da ita kuma macen za'a ɗaura mata aure a watan Disamba.
Asali: Legit.ng