Babbar magana: 'Yan bindiga sun kai wa 'yan sanda wasikar sanarwar kai hari a Zamfara
- Bayan kai wasikar sanar da kai hari ga coci a jihar Zamfara, 'yan bindiga sun mika wa rundunar 'yan sanda wasika
- Rundunar 'yan sanda ta tabbatar da kai wasiku ga coci a jihar, inda rundunar ta bayyana matakin da za ta dauka
- Kwamishinan 'yan sandan jihar tuni ya ba da umarnin a ci gaba da sanya ido a coci da masallatai a jihar
Zamfara - Rundunar ‘yan sandan jihar Zamfara ta tabbatar da cewa ta samu wasikar barazanar kai hari a wani coci-coci a Gusau, babban birnin jihar.
Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Ayuba Elkanah, ya ce wasu da ba a san ko su wanene ba ne suka jefar da wasikar a hedikwatar ‘yan sandan jihar.
Ya bayyana hakan ne a wata tattaunawa da manema labarai a Gusau ranar Talata, SaharaReporters ta ruwaito.
A cewarsa, har yanzu ‘yan sanda ba su tabbatar da wadanda suka rubuta wasikar ba. Sai dai rundunar ‘yan sandan ta tabbatar wa mabiya addinin Kirista a jihar cewa ‘yan sanda za su ba su isasshen tsaro.
A cewarsa:
“Har yanzu ba mu san daga inda wasikar ta fito ba, amma duba da halin da kasar nan ke ciki, ba za mu zauna mu nade hannu da abin da wasikar ta kunsa ba.
“Za mu samar da isasshen tsaro ga dukkan coci-coci da ma masallatai a lokutan gudanar sallah da hidiman coci.
"Na ba da umarnin a tura isassun jami'an tsaro zuwa coci-coci da ma masallatai daga ranar Juma'a mai zuwa."
A rahoton gidan talabijin TVC, Legit.ng Hausa ta gano hotunan wasikar, duk da cewa rubutun jikin wasikar bai fito da kyau ba.
'Yan bindiga sun rubuta wa kiristocin Zamfara wasika
Idan baku manta ba, wasu kungiyoyin yan bindiga sun rubuta wa kiristocin jihar Zamfara, Arewa maso yammacin Nigeria waska sun umurci su rufe coci-cocinsu idan ba haka ba su kai musu hari, SaharaReporters ta ruwaito.
Rundunar yan sandan jihar Zamfara sun tabbatar wa SaharaReporters da wannan barazanar inda suka ce, 'Muna bincike kan barazanar.
Mai magana da yawun yan sandan jihar, DSP Mohammed Shehu, ya shaida wa wakilin majiyar Legit.ng cewa sun san da wasikar barazanar.
Asali: Legit.ng