Yanzu-yanzu: Kwale-kwale ya kife da daliban Islamiyya a jihar Kano, mutum 20 sun mutu

Yanzu-yanzu: Kwale-kwale ya kife da daliban Islamiyya a jihar Kano, mutum 20 sun mutu

  • Kwale-kwale ya kife da daliban Islamiyya dake hanyar zuwa Malulidi jihar Kano
  • An tsinci gawar mutum 20 kuma mutum 7 sun tsira

Kano - Kwale-kwale ya kife da Fasinjoji kimanin 47 ciki har da daliban makarantar Madinatu Islamiyya dake karamar hukumar Bagwai ta jihar Kano.

Daily Trust ta ruwaito cewa kwale-kwalen ya kife ne a hanyar zuwa Bagwai dake Badau.

Rahoton ya kara da cewa daliban na hanyarsu ta zuwa bikin Maulidi ne don murnar ranan haihuwan Manzon Allah (SAW).

Wata majiyar ya bayyana cewa sama da fasinjoji 40 wannan abu ya shafa,

Majiyar, wacce ke asibitin Bagwai ta bayyana cewa kawo yanzu an ga gawawwakin mutum 20 kuma an ajiyesu a dakin ajiye gawawwaki.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kara karanta wannan

Tashin Hankali: An tsinci gawar wani mutumi mai aure, da wata Amarya a cikin mota a Kano

Yanzu-yanzu: Kwale-kwale ya kife da daliban Islamiyya a jihar Kano, mutum 20 sun mutu
Yanzu-yanzu: Kwale-kwale ya kife da daliban Islamiyya a jihar Kano, mutum 20 sun mutu

An ceto mutum 7, an tabbatar da mutuwar 20

Kakakin hukumar kwana-kwanan jihar Kano, Saminu Abdullahi, ya ce da misalin karfe 9:15 na dare an tura jami'ai kai dauki, Daily Trust ta jiyo.

Ya tabbatar da labarin cewa an gano gawawwaki 20.

Ya yi karin bayanin cewa kwale-kwalen na dauke da mutum 47.

Yace:

"A yanzu da muke magana jami'an kai dauki sun gano gawawwaki 20 kuma sun tsinci mutum 7 da rai."

Mummunan hatsarin mota ya laƙume rayukan mutum 15 a Jigawa

Rundunar yan sandan Nigeria reshen jihar Jigawa ta ce a kalla mutane 15 ne suka riga mu gidan gaskiya sakamakon mummunan hatsarin mota da ya faru a jihar.

Mai magana da yawun yan sandan jihar, Lawan Shiisu, a ranar Litinin a garin Dutse ya ce hatsarin ya faru ne a hanyar Achlafiya zuwa Karnaya, The Nation ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Hanyoyi 5 da za'a ka iya kare ban dakin zamani daga macizai

ASP Shiisu ya ce motoci biyu ne hatsarin ya ritsa da su misalin karfe 5 na yamma a karamar hukumar Yan Kwashi na jihar.

Ya ce:

"Motoccin biyu sun hadu ne gaba da gaba, sun yi karon ne yayin da daya daga cikinsu ya ke kokarin kaucewa rami a titin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng