Babbar Magana: Tsagerun yan bindiga ka iya lalata sabbin jiragen Super Tucano a jihar Neja

Babbar Magana: Tsagerun yan bindiga ka iya lalata sabbin jiragen Super Tucano a jihar Neja

  • Majalisar wakilan tarayyan Najeriya ta yi kira ga gwamnati ta ɗauki matakin kare wurin da aka aje sabbin jiragen Super Tucano
  • Dan majalisa mai wakiltar mazabar Agwara/Borgu a jihar Neja, Jafaru Muhammed, ya bayyana hatsarin da jiragen ke ciki
  • Yace duba da yawaitar hare-haren yan bindiga a mazaɓarsa, jiragen na fuskantar barazanar hari da lalatawa

Niger - Dan majalisar wakilan tarayya mai wakiltar mazaɓar Agwara/Borgu, Jafaru Muhammad (APC, Niger), yace sabbin jiragen da Buhari ya siyo na fuskantar barazana a Neja.

Dailytrust ta rahoto cewa Jiragen yakin Super Tucano da aka aje a sansanin sojojin sama na 407 dake Sabuwar Bassa da sauran makaman yaki na fuskantar barazanar harin yan bindiga, inji dan majalisan.

Super Tucano
Babbar Magana: Tsagerun yan bindiga ka iya tarwatsa sabon jirgin yakin Super Tucano a Neja Hoto: Do You Know NG FB Fage
Asali: UGC

Honorabul Jafaru ya yi wannan furucin ne a zaman majalisar wakilai na yau Talata 30 ga watan Satumba.

Kara karanta wannan

Yan bindiga da Sojojin sun yi musayar wuta a Imo kan umarnin zama a gida na IPOB

Da yake jawabi kan kudirin da ya gabatar, ɗan majalisan ya yi kira ga gwamnatin tarayya ta kara zage dantse wajen magance ayyukan yan bindiga a yankunan mazaɓarsa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Yace:

"Sabbin jiragen yakin Super Tucano da gwamnati ta aje a makarantar koyon sarrafa makamai ta sama ta 407 dake Sabuwar Bassa, suna fuskantar hatsarin hari da lalata su."
"Sabida wurin na da kusanci da sansanin yan bindiga na filin kiyo na Kaiji dake yankin Burgu."
"Hakanan kuma gidan gyaran hali dake Bataliyar sojoji ta 221 da 101 na tsare da wasu yan ta'addan kungiyar Boko Haram, kuma hakan barazana ce ga rayuka da dukiyoyin al'ummar dake rayuwa a yankin."

Yan bindiga suna yawaita kai hari yankin

Dan majalisan ya kuma bayyana cewa yan bindiga sun matsawa mutane dake yankin Babanna da Malale, wasu sassan Wawa, Shagunu da Pissa/Kabe a karamar hukumar Borgu.

Kara karanta wannan

Innalillahi: Dan majalisar dokoki na jam'iyyar APC ya riga mu gidan gaskiya

Ya kuma roki gwamnatin tarayya ta kara tura dakarun soji bataliya ta 101, 221 da kuma makarantar koyon sarrafa makamai dake Wawa domin tsare rayuka da dukiyoyin al'umma.

A wani labarin kuma An harbe kasurgumin dan bindigan da ya jagoranci sace matafiya a hanyar Kaduna-Abuja

Rahotanni sun bayyana cewa jami'an hukumar yan sanda ne suka wa tawagarsa kwantan bauna yayin da suka je siyan barasa a cikin Kaduna.

Yan bindigan sun kwashe kwanaki hudu suna kai hari a lokuta daban- daban a kan hanyar Kaduna zuwa Abuja.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262