'Yan sanda sun hana 'yan ta'addan Boko Haram sace soja da fasinjoji 15 a Borno
- Jami'an yan sandan Najeriya sun taka wa wasu gungun yan ta'addan Boko Haram birki a Yanakari/Kondori, Jihar Borno
- Yan ta'addan cikin motocci kimamin 20 masu bindiga sun tare hanya ne da niyyar sace fasinjoji ciki har da soja
- Nan take jami'an yan sandan suka amsa kirar gaggawa suka kuma fatattaki yan ta'addan suka ceto fasinjoji da sojan
Jihar Borno - Jami'an yan sanda sun hana wasu da ake zargin yan Boko Haram ne sace wani jami'in soja a jihar Borno, majiyoyi suka shaidawa The Cable.
Sojan, wanda ke aiki a bataliyar sojoji da ke Marte, yana kan hanyarsa daga Damaturu zuwa Maiduguri ne lokacin da yan ta'addan suka kai hari.
Nasara daga Allah: Sabon Jirgin yaƙin Super Tucano ya yi ɓarin wuta kan yan ta'ddan Boko Haram da ISWAP a Gajiram
Majiyoyi sun ce yan sandan sun kuma hana yan ta'addan sace wasu fasinjoji guda 15, The Cable ta ruwaito.
Lamarin ya faru ne a kusa da kauyukan Yanakari/Kondori a kan hanyar.
Motocci suna zuwa ne daga garuruwa daban-daban domin shiga Maiduguri, da isarsu wurin sai yan ta'addan suka yi yunkurin su sace su.
Yan sandan, wasu cikinsu daga tawagar agajin gaggawa ta RRS, sun isa wurin nan take sannan suka yi musayar wuta da yan ta'addan, suka ceto wasu da aka sace.
Wani babban majiya daga yan sanda ya ce:
"Yan ta'addan sun taho ne cikin motocci masu bindiga kimanin 20."
"Sojan, da ya karbi izinin tafiya gida, shima yana cikin wani motar fasinjoji ne a yayin da yan ta'addan suka kai harin.
"Tawagar yan sandan sun fatattake su, inda suka tsere cikin daji. Da farko sojan ya shige daji da gudu, amma daga baya ya fito bayan yan sandan sun iso."
Rundunar yan sandan ba ta iya bata karin haske ba a kan lamarin a halin yanzu.
Yayin da sojoji ne kan gaba wurin yaki da yan ta'addan, yan sanda suma suna bada taimakon su.
Rahoto: Masu ƙera wa Boko Haram bama-bamai sun koma dazukan Kudancin Kaduna
A jiya, kun ji cewa shugabannin kungiyar Boko Haram da ke biyayya ga Bakoura Buduma sun mayar da masu hada musu bama-bamai dazukan yankin kudanci Kaduna, a cewar wani rahoton da PRNigeria ta fitar.
A baya-bayan nan ne aka mayar da masu hada bama-baman da ake kira Amaliyyah a tsakin 'yan ta'addan, zuwa Rijana, Igabi da Chikun a yankin kudancin Kaduna.
Majiyoyi daga ciki sun ce kungiyoyin biyu na Boko Haram za su yi amfani da duwatsun da ke yankin a matsayin mabuya.
Asali: Legit.ng