FG ta zargi ESN da yanka wasu ‘yan sanda tare da yada bidiyon gawarwakinsu a intanet
- Gwamnatin tarayya ta zargi kungiyar ta'addancin nan ESN a kudu maso gabas da kashe ‘yan sanda biyu a jihar Anambra
- A cewar gwamnatin, ‘yan kungiyar ‘yan bindigan ba wai kashe ‘yan sandan kawai suka yi ba, har ma sun dauki bidiyon ta'addancin
- Gwamnati ta sha alwashin bin diddigin wadanda suka yi kisan a yayin da take yiwa ‘yan sandan da aka yi wa kisan gill addu'a
Gwamnatin tarayya ta zargi kungiyar tsaro mai alaka da IPOB ta Eastern Security Network (ESN) da kashe ‘yan sanda biyu a jihar Anambra.
Zargin na kunshe ne a wata sanarwa da ministan yada labarai da al’adu na Najeriya, Lai Mohammed ya aikewa majiyar Legit.ng a ranar Litinin, 29 ga watan Nuwamba.
Gwamnati ta yi gargadin cewa za a kama wadanda suka aikata kisan, suka dauki hoton danyen aikin da suka aikata, suka yada irin wannan abu, kuma za a gurfanar da su a gaban kuliya.
ESN kungiya ce da ke daukar makamai masu alaka da kungiyar Indigenous People of Biafra (IPOB), kungiyar masu fafutukar ballewa a yankin kudu maso gabas a Najeriya.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Wani bangare na sanarwar ya bayyana cewa:
“Muna da sahihan bayanai cewa ASP Francis Idoko (AP No. 154945); Sufeto Emmanuel Akubo (AP No. 222336) da Insfekta Rufa’i Adamu (AP. 285009), dukkansu jami’an ‘yan sandan Najeriya ne, ‘yan kungiyar ESN sun yi garkuwa da su, bisa umarnin shugabansu, Chinonso Okafor, wanda aka fi sani da TEMPLE a ranar 27 ga Nuwamba, 2021.
“An kashe biyu daga cikin jami’an, Insifekta Akubo da Adamu ta hanya mafi muni kuma an yi faifan bidiyo da ke ta yawo yana nuna gawarwakinsu da aka yanka. Shugaban tawagar ESN da ya kashe jami'an biyu wani mai suna 'GENTLE'.
"Chinonso Okafor, babban kwamandan ESN mai kula da jihohin Imo da Anambra, da kuma 'Gentle' da duk wadanda suka aikata wannan mugun aiki za su fuskanci hukunci cikin gaggawa."
Lai Mohammed ya ce hari da kashe jami’an tsaro, ta ko wane fanni, hari ne kai tsaye ga kasa baki daya, kuma ba za a amince da shi ba.
Yayin da IPOB da ESN ke ci gaba da aikata barna, dattawan Arewa sun shawarci shugaba Buhari kan cewa kada ya saki Nnamdi Kanu.
Sun bayyana cewa, ya kamata a bar doka tayi abin da ya dace kan Nnamdi Kanu, kana ya yi watsi da bukatar dattawan Igbo na yafe wa Kanu.
Bukatar sakin Nnamdi Kanu babban lamari ne, amma zan yi shawara: Buhari ga Dattawan Igbo
A wani labarin, Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana cewa sakin Nnamdi Kanu, shugaban kungiyar yan ta'addan IPOB ya sabawa dokar da ta baiwa sashen Shari'a karfin cin gashin kanta.
Buhari ya bayyana hakan yayinda ya karbi bakuncin manyan dattawan Igbo wanda ya hada da Tsohon Minista Sufurin Sama kuma tsohon dan majalisa, Chief Mbazulike Amaechi.
Mai magana da yawun Shugaban kasa, Femi Adesina, ya bayyana hakan a jawabin da ya saki ranar Juma'a.
Asali: Legit.ng