Bidiyon tankar mai da ta fadi ta fashe, ta kashe mutane da yawa a jihar Ogun
- Wata babban tankar mai ta fadi ta kuma fashe a wani yankin jihar Ogun da sanyin safiyar yau ranar Lahadi
- Rahotanni da muke samu sun bayyana cewa, wasu adadin mutane sun mutu, wanda har yanzu ba a tantance ba
- Hukumomin tsaro sun tabbatar da faruwar lamarin, inda suka bayyana kokarin da suke na shawo kan lamarin
Ogun - Ana fargabar mutane da dama sun mutu bayan da wata tankar mai dauke da man fetur ta fashe a kusa da Oju Irin da ke unguwar Lafenwa a Abeokuta ta jihar Ogun.
TheCable ta ruwaito cewa, ta samu labarin cewa fashewar ta faru ne da safiyar yau Lahadi 28 ga watan Nuwamba, 2021.
Mutanen da ba a tantance adadinsu ba ne gobarar ta shafa, da suka hada da shaguna da gine-ginen da ke kewaye da yankin.
Babatunde Akinbiyi, mai magana da yawun hukumar kula da zirga-zirgar ababen hawa (TRACE), ya tabbatar da faruwar lamarin.
Akinbiyi ya ce tankar ta fashe ne sakamakon rashin hadin kai da mutanen da ke kusa suka nuna, inda ya ce suna kwashe man fetur ne, lamarin da ya janyo gobarar.
Ya ce, motar ta dakon mai, ta kife ne da misalin karfe 4:45 na safe, yayin da take kan hanyarta ta zuwa Rounder daga Oju-Irin, Lafenwa, lamarin da ya sa mai ya zube a kan titi.
Ya bukaci mazauna yankin da su fice daga wajen, inda ya ce TRACE, ‘yan sanda, hukumar kiyaye hadurra ta kasa (FRSC) da hukumar kashe gobara suna nan a shirye domin shawo kan lamarin.
Ya kara da cewa:
“Bugu da kari, jama’a masu motoci da ke shiga yankin Rounder daga Lafenwa, ya kamata su yi amfani da hanyar Olomore da Oke-Ata a matsayin zabi, tunda an karkatar da ababen hawa daga wurin da lamarin ya faru."
Kakakin ya ce za a yi karin bayani ga manema labarai nan ba da jima wa ba.
Shi ma kwamandan hukumar FRSC a jihar Ahmed Umar ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce jami’an hukumar na nan a shirye domin kula da ababen hawa.
A cikin wani bidiyo da Legit.ng Hausa ta samo daga jaridar Daily Trust, an hango hayakin da ke nuna alamar wuta na ci a inda tankar ta fadi.
Kalli bidiyon:
Bayan rugujewar gini, mummunar gobara ta kone gine-gine a Legas
A wani labarin, an samu hargitsi a ranar Laraba, 3 ga watan Nuwamba, yayin da wata gagarumar gobara ta cinye wasu gine-gine da shaguna a Owode Onirin, daura da unguwar Ikorodu Road a Legas.
Vanguard ta rahoto cewa a lokacin da jami’an hukumar kashe gobara ta jihar Legas, suka isa wurin da lamarin ya faru, wasu fusatattun matasa sun far musu.
An ce matasan sun kai wa jami’an hari ne saboda rahotanni sun ce sun isa wurin a makare bayan an yi ta kiran su yayin da wutar ta kama.
Asali: Legit.ng