An dakatad da Shugaban APC a Anambra kan laifin 'ya yiwa Buhari rashin kunya
- Da alamun sabon rikici ya kunno kai cikin jam'iyyar APC a jihar Anambra bayan shan kaye a zaben gwamnan jihar
- A farkon watan nan, jam'iyyar ta sanar da dakatad da Kakakinta, Okelo Madukaife, kan laifin yi wa jam'iyya zagon kasa
- Yanzu kuma an sanar da dakatad da Shugaban jam'iyyar da kansa
Awka - Jam'iyyar All Progressives Congress (APC), shiyar jihar Anambra a ranar, 25 ga Nuwamba ta sanar da dakatad da shugabanta, Cif Basil Ejidike.
Jaridar The Nation ta ruwaito cewa jam'iyyar APC ta bayyana cewa ta dakatad da shugabanta ne bisa zargin saba umurni da kuma rashin kunya ga ofishin Shugaban kasa Muhammadu Buhari.
Sabon shugaban rikon kwarya na jam'iyyar a Anambra, Okonkwo Okom, ya bayyanawa manema labarai a Awka cewa an yanke shawarar dakatad da Cif Basil ne a taron shugabanni da masu ruwa da tsaki a jam'iyyar.
Ya ce cikakken bayani kan dalilan da yasa suka dakatad da shi na kunshe cikin karar da aka shigar kansa ga uwar jam'iyya don yanke masa hukunci.
Martanin Shugaban da aka dakatar
Ejidike ya bayyanawa Jaridar Vanguard a hira cewa Okom da wadanda suka dakatad da shi basu da hurumin yin hakan.
Ya zargesu da cewa ba yan jam'iyya bane, ta yaya zasu koreshi daga jam'iyya.
A cewarsa:
"Ba mambobin jam'iyyarmu bane. Wasu yan yawo ne da suka fita daga jam'iyyar bayan zaben fidda gwani. Ba zasu iya dakatad da ni ba, ina hedkwatar uwar jam'iyya a Abuja."
Zaben Anambra: Ni fa ban yarda na fadi zabe ba, zamu hadu a kotu - Andy Uba na APC
Dan takaran jam'iyyar All Progressives Congress (APC) a zaben gwamnan Anambra da aka kammala, Andy Uba, yace sam ba yarda da sakamakon zaben da INEC ta sanar ba.
A cewarsa, ta yaya zai fadi a zabe a gundumomin da shugabannin APGA suka koma APC ana saura mako daya zabe.
Andy Uba ya bayyana haka ne ranar Asabar yayinda jawabi ga mambobin jam'iyyar APC, rahoton DailyTrust.
Ya lashi takobin cewa zai kai kara kotun zabe.
Asali: Legit.ng