Da Dumi-Dumi: Tsagerun yan bindiga sun yi awon gaba da shugaban makaranta, mataimaki da malamai uku

Da Dumi-Dumi: Tsagerun yan bindiga sun yi awon gaba da shugaban makaranta, mataimaki da malamai uku

  • Wasu yan bindiga da ake zargin masu garkuwa ne sun sace shugaban makaranta, mataimakinsa da wasu malamai uku
  • Rahotanni sun bayyana cewa maharan sun farmaki malaman ne ba zato yayin da suke kan hanyar komawa gida daga makaranta
  • Lamarin da ya faru a jihar Ondo, tuni yan sanda suka bazama cikin jeji domin ceto mutanen da aka sace

Ondo - Wasu da ake zaton masu garkuwa ne sun sace shugaban makaranta, Joshua Adeyemi, mataimakinsa, lfedayo Yesufu, da wasu malamai uku a kan hanyar Auga-Ise, jihar Ondo.

Vanguard ta rahoto cewa Mista Adeyemi, shine shugaban Auga Community Grammar School, yayin da lfedayo ne mataimakinsa.

Hakanan kuma malamai ukun da aka sace duk daga makarantar suka hito, Oloyede Bukola, Adagunodo Funmilayo da kuma Blessing Okeke.

Yan bindiga
Da Dumi-Dumi: Tsagerun yan bindiga sun yi awon gaba da shugaban makaranta, mataimaki da malamai uku Hoto: punchng.com
Asali: UGC

A ina maharan suka sace su?

Kara karanta wannan

Ana daf da yi musu yankan rago: Amotekun sun ceto makiyaya fulani 2 da wasu fulanin suka yi garkuwa da su

Wani shaidan gani da ido yace lamarin ya faru ne ranar Alhamis da yamma, yayin da suke tafiya a motar shugaban Toyota Corolla a kan hanyar Auga-Ise.

Mutumin ya bayyana cewa ba zato maharan suka farmake su, sannan suka tasa keyarsu zuwa cikin jeji.

Maharan sun sako ɗaya daga cikin malaman da suka sace, Blessing Okeke, saboda sun gano tana ɗauke da juna biyu.

Yadda lamarin ya faru

Da take zayyana yadda lamarin ya auku, Blessing tace maharan sun farmake su yayin da suke kan hanyar komawa gida daga makaranta a cikin motar shugaban makaranta.

Blessing ta bayyana cewa sun yi tafiya ta tsawon awanni a cikin jeji kafin yan bindigan su sallame ta bayan sun gano tana da ciki.

Wane matakin yan sanda suka ɗauka?

Kara karanta wannan

Tashin Hankali: An tsinci gawar wani mutumi mai aure, da wata Amarya a cikin mota a Kano

Shugaban ofishin yan sanda na Ikare, DPO Oladutoye Akinwan, yace tuni aka tura jami'an yan sanda su mamaye jejin domin ceto mutanen da aka sace.

Akinwa ya kara da cewa jami'ai sun ɗakko motar da malaman ke ciki kafin maharan su tasa keyar su zuwa jeji, kamar yadda Punch ta ruwaito.

A wani labarin na daban kuma yan binidga sun gargaɗi iyalan dan sanda su gaggauwa kawo miliyan N200m kafin su bar wurin sabis

Yan bindigan da suka sace matafiya a kan hanyar Kaduna zuwa Abuja sun nemi iyalan wani ɗan sanda su biya fansa.

Rahoto ya bayyana cewa maharan sun nemi a tattara musu miliyan N200 cikin awanni 6 kafin su bar gurin sabis.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262