Shaidar EFCC: Da kaina na ciro wa Jang biliyoyin naira babu takarda
- Shaidar EFCC ta sanar da yadda tsohon gwamna Jonah Jang na jihar Filato ya dinga wafce kudaden jihar babu takardar dalilin hakan
- Habila Dung, wanda tsohon sakataren gwamnatin jihar ne, ya sanar da yadda Jang ya umarcesa ya cire har N4 biliyan a cikin watanni 5
- A cewarsa, ana amfani da sunan manyan ayyuka ne wurin cire kudaden amma babu bayanin yadda za a kashe kudaden sai su kare a aljihun gwamnan
Filato - Wani shaidar da hukumar yaki da rashawa tare da hana yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa, Habila Dung, ya bayar da labarin yadda tsohon Gwamna Jonah Jang ya umarcesa da ya shirya fitar da N4 biliyan tsakanin watan Janairu zuwa Mayun 2015.
Dung, wanda babban sakatare ne a ofishin gwamnan tsakanin 2014 da 2015, ya sanar da babban kotun jihar Filato cewa babu wata takarda da ake amfani da ita wurin cire kudaden da Jang ya dinga halakawa yayin da ya ke ofishin gwamnan, Daily Trust ta ruwaito.
Tsohon sakataren gwamnatin ya ce, "Ofishin sakataren gwamnatin jihar ya na da asusu biyu da wani banki. Asusun farkon na 'yan majalisa ne da masu bada shawara na musamman, sai na biyun kuma na manyan 'yan siyasa ne.
“Masu saka hannu a cire kudi su ne manyan sakatarorin gwamnatin jihar biyu da kuma daraktan kudi," ya kara da cewa.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Dung ya ce dukkan bukatar fitar da kudi da Gwamna Jonah Jang ya mika kuma kashiya Yusuf Gyang Pam ya fitar an yi da sunan manyan ayyuka ne, Daily Trust ta ruwaito.
Dung ya kara da sanar da kotun cewa, a ranar 8 ga watan Afirilun 2015, mutum na biyu da ke kare kansa ya fitar da kudi har N700 miliyan.
Ya ce, "Ban san yadda gwamnan ya kashe kudin ba bayan ya kai masa."
A ranar Laraba, wata shaidar EFCC ta sanar da kotun kan yadda tsohon gwamnan ya cire N1.9bn a cikin wata biyar.
EFCC ta gurfanar da mataimakin ma'ajin jami'ar ABU kan zargin wawurar N6m
A wani labari na daban, hukumar yaki da rashawa ta EFCC ta gurfanar da mataimakin ma’ajin jami’ar Ahmadu Bello, Iliyasu Abdulrauf Bello gaban alkali Darius Khobo na babbar kotun jihar Kaduna bisa zarginsa da kwasar N6,000,000.
Iliyasu na rike da kujerar mukaddashin shugaban kungiyar manyan ma’aikatan jami’ar, SSANU, reshen jami’ar. Ana zarginsa da wawurar wasu kudade daga asusun kungiyar da aka ware don walwalar ma’aikatan.
Bincike ya nuna yadda aka dinga wawurar kudade daga cikin asusun kungiyar ba tare da mambobin kungiyar sun sani ba.
Asali: Legit.ng