Takaddama ta barke tsakanin malaman musulunci da iyalan jarumin fim a wajen binne shi
- An samu yar takaddama tsakanin malaman musulunci da iyalan jarumin fim da ya rasu a wajen binne shi
- Malaman dai sun nuna rashin dadi a kan wasu abubuwa da iyalan marigayin da masoyansa suka dunga yi wanda baya bisa tsarin Musulunci
- Daga cikin abun da iyalan suka yi shine sanya gawar mamacin a cikin akwati da kuma jinkiri wajen binne shi
An samu yar sabani tsakanin malaman Musulunci da iyalan marigayi dan wasan Nollywood, Babatunde Omidina wanda aka fi sani da Baba Suwe lamarin da ya kawo jinkiri wajen binne shi.
Ranar Alhamis, 25 ga watan Nuwamba, aka tsayar domin binne marigayin a gidansa da ke yankin Ikorodu ta jihar Lagas, jaridar The Nation ta rahoto.
Dandazon jama'a sun taru a safiyar yau a gidan nasa da ke Ikorodu domin samun jana'izar marigayi dan wasan.
Malamin, Sheikh Ahamad Olanrewaju Alfulanny, wanda ya zanta da jaridar The Nation, ya nuna rashin gamsuwa da abubuwan da iyalan da sauran abokan arziki suka yi wanda ya sabawa koyarwar Musulunci.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Ya bayyana cewa a koyarwar Musulunci, a kan binne mamaci cikin yan sa'o'i kadan bayan tabbatar da mutuwarsa.
Ya ce koda dai Baba Suwe, ya kasance shahararren jarumi a lokacin da yake raye, addinin Musulunci bai bayar da damar yin wasu surkulle a yayin binne gawa ba.
Malamin ya ce:
"Akwai abubuwa da dama da suke yi, wanda baya bisa tsarin addinin Musulunci, sun sanya gawarsa a cikin akwati, wasu abokan arziki har cewa suka yi za su zagaya da gawarsa, amma iyalan sun fada mana cewa ba za su binne shi da akwatin ba."
Masu fatan alkhairi, masu makoki basu ji dadin hukuncin ba amma malaman sun ce iyalan sun amince za su bi koyarwar addinin Musulunci.
Fitaccen jarumin Nollywood, Baba Suwe, ya mutu
A baya mun kawo cewa, tsohon jarumin fina-finan Nollywood da Yarbanci, Babatunde Omidina da aka fi sani da Baba Suwe ya riga mu gidan gaskiya.
The Nation ta ruwaito cewa ya mutu ne a ranar Litinin yana da shekaru 67 a duniya.
Yarsa mai suna Adesola Omidina ce ta sanar da rasuwar baba Suwe.
Asali: Legit.ng