Yayin da soji suke lugude kan Boko Haram a Malam Fatori, 'yan ta'adda sun mika makamansu a Gwoza
- Sojojin Najeriya suna tsaka da luguden wuta a kan 'yan ta'addan Boko Haram a Malam Fatori, wasu 'yan ta'addan sun mika wuya a garin Gwoza
- Wannan al'amarin ya faru ne a ranar Laraba yayin da wasu kwamandoji da mayakan Boko Haram suka tsere daga dajin Sambisa da ke Borno
- Duk da kokarin dakile su da aka yi a yankin Jaje na dajin, sun garzaya titin Limankara da ke Borno inda suka ce akwai wasu da za su mika makamai
Borno - Wasu mayakan Boko Haram sun mika wuya tare da ajiye makamansu a ranar Laraba a garin Gwoza yayin da dakarun sojin Najeriya ke tsaka da ruwan wuta a kan wasu 'yan ta'addan a Malam Fatori da yammacin Laraba.
Nasrun minallah: Jirgin yakin sojoji ya yi luguden wuta kan masu karban haraji na kungiyar ISWAP a Borno
Duk da 'yan ta'addan ISWAP sun so hana hakan, kwamandojin Boko Haram da wasu mayakansu sun mika makamansu ga sojojin.
Wata majiyar tsaro ta sanar da PRNigeria cewa, mayakan Boko haram masu yawa za su mika makamansu kafin shekarar nan ta kare.
"Wasu tsoffin kwamandojin Boko Haram da mambobinsu sun tsero daga yankin Jaje da ke dajin Sambisa kuma da kansu suka mika wuya ga sojojin rundunar Operation Hadin Kai ta bataliya ta 192 da ke kan titin Gwoza zuwa Limankara a jihar Borno.
"A halin yanzu, sama da mambobi 17,000 na Boko Haram ne suka mika wuya duk da kokarin da ISWAP ke yi na hana hakan," jami'in yace.
A daya bangaren, PRNigeria ta tattaro cewa, dakarun sojin Najeriya a ranar Laraba sun yi musayar wuta da 'yan ta'addan ISWAP a Malam Fatori.
Da Duminsa: Masu garkuwa sun kashe tsohon mai neman takarar gwamnan Zamfara a hanyar Abuja zuwa Kaduna
Malam Fatori na daya daga cikin garuruwan da 'yan ta'addan ISWAP suka mamaye kuma suka kafa kwamitin Shura. Garin ya na kusa da iyakar jamhuriyar Nijar.
A ranar 3 ga watan Nuwamba, PRNigeria ta ruwaito yadda mayakan ISWAP suka kai farmakin ba-zata kuma suka halaka jami'an tsaron hadin guiwa da suka fito aiki.
Gwamnan jihar Borno, Babagana Zulum ne ya shirya aikin 'yan sintirin domin dubawa tare da tantance gidajen da 'yan gudun hijira suka tsere daga Abadam zuwa Nijar suka bari.
ISWAP sun tilasta wa manoman kauyukan Borno biyan haraji, sun ce zakkar gona ce
A wani labari na daban, jama'a masu zama wasu daga cikin kauyukan Borno sun koka da halin da suka samu kansu na tilascin biyan haraji da 'yan ta'adda suka saka musu a cikin zakkar amfanin gona.
Kamar yadda BBC ta wallafa, jama'a mazauna garin Damboa sun sanar da yadda 'yan ta'addan ke amfani da karfi wurin kwace amfanin gona da dabbobi, kuma biyayya a gare su ta zama dole domin tsira.
Wannan al'amarin ya kara fitowa ne a lokacin da ake cigaba da rade-radin cewa 'yan ta'addan ISWAP na amshe haraji daga wurin makiyaya da manoman jihar Borno.
Asali: Legit.ng