Hotunan Kakakin majalisar dokokin jiha da zai Angonce da kyakkyawar Amaryarsa
- Kakakin majalisar dokokin jihar Oyo, Honorabul Adebo Ogundoyin, zai angonce da masoyiyarsa Olamidum Majekodunmi
- Rahoto ya tabbatar da cewa za'a fara shagalin bikin jigon siyasan ne daga ranar Alhamis 25 ga watan Nuwamban wannan shekaran
- Bikin wanda za'a shafe kwanaki ana yinsa, an sa ran zai samu halartan manyan jiga-jigan siyasa a ƙasar nan
Oyo - Kakakin majalisar dokokin.jihar Oyo, Honorabul Adebo Ogundoyin, zai Angonce da masoyiyar amaryarsa, Miss Olamidun Majekodunmi.
Dailytrust ta ruwaito cewa Amarya da Angon sun bayyana hotunan su na kafin aure wato Pre-Wedding ranar Laraba.
Rahotanni sun tabbatar da cewa za'a gudanar da bikin ɗaura aure ne daga ranar 25 ga watan Nuwamba, zuwa ranar 27 ga watan Nuwamba, 2021.
Hotunan kafin Aure na masoyan guda biyu
Shagalin bikin wanda za'a fara gobe Alhamis, 25 ga watan Nuwamba, ana tsammanin halartan manyan jiga-jigan siyasan ƙasar nan.
Daga cikin irin manyan mutanen da ake tsammanin zuwansu Ibadan babban birnin jihar Oyo, akwai tsohon shugaban ƙasa, Olusegun Obasanjo, tsohon mataimakin shuagaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar.
Kazalika ana ganin kusan gwamnonin 13 ne zasu halarci bikin daga sassa daban daban na kasar nan, da kuma sarakunan gargajiya.
A wani labarin na daban kuma Maganar Gwamna El-Rufa'i na rokon yan Najeriya kada su zabi PDP a 2023 ya bar baya da kura
Gwamnan Kaduna ya roki yan Najeriya musamman mutanen jihar kada su kuskura su zabi jam'iyyar PDP a 2023.
Sai dai wannan magana ba tai wa yan Najeriya dadi ba, inda tuni wasu suka fara sukar gwamnan.
Asali: Legit.ng