Bidiyon Macijiyar da ta hallaka jami'ar Soja cikin ban daki a Abuja

Bidiyon Macijiyar da ta hallaka jami'ar Soja cikin ban daki a Abuja

  • Macijiyar da ta yi sanadiyyar mutuwar wata hafsar Sojin saman Najeriya a birnin tarayya Abuja ta shiga hannu
  • Mai kamen maciji ya shiga cikin bayin ya fito da bakar macijiyar daga cikin masai
  • Mutane da dama sun tofa albarkatun bakinsu kan wannan abin takaici

FCT Abuja - An damke macijiyar da tayi sanadiyar mutuwar jami'ar hukumar Sojin saman Najeriya, Lance Kofur, Bercy Ogah, a barikin NAF Base dake birnin tarayya Abuja.

Wani bidiyon da Daily Trust ta wallafa ya nuna yadda wani mai kamen maciji ya fito da macijiyar cikin masai.

A bidiyon, a kan ji yadda mutanen da ke wajen suka kira ga a kashe macijiyar.

Kalli bidiyon:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kara karanta wannan

Tuɓe wa ɗaliba hijabi a bainar jama'a: Farfesa Lawal ya bada haƙuri bayan ƙungoyoyin musulmi sun yi ca a kansa

Jami'ar Soja ta gamu da cizon macijiya cikin ban dakin gidanta dake barikin Soji, ta mutu

Jami'ar hukumar mayakan saman Najeriya, Lance Kofur Bercy Ogah, ta gamu da ajalinta cikin ban daki yayinda macijiya ta cijeta a gidanta.

Jami'ar ta fuskanci cizon macijiyar ne yayinda take biyan bukatarta a bayin gida cikin barikin Sojin NAF Base dake Abuja.

Punch ta ruwaito cewa bayan cizon, Kofur Ogah ta kwashe yaran dake gidanta kuma ta kaisu wajen makwabta sannan ta garzaya asibitin Nigerian Air Force hospital amma lokaci ya yi.

A rahoton, wannan abu ya auku ne da safiyar ranar Juma'a.

Me ya faru da taje asibiti?

Majiya ta bayyana cewa jami'ar ta mutu a asibitin ne saboda dalilai da dama wanda ya hada da rashin duba ta da wuri.

A cewar majiyar:

"Da ta isa asibiti, sai da aka dau lokaci kafin yi mata allurar maciji. Bayan rashin magani, na samu labarin cewa wanda ke da hakkin bada magunguna ba ya nan."
"Hakazalika sashen jikin da macijin ya cijeta na cikin dalilan da yasa ta mutu."

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng