Gwamnan Nigeria ya ce jiharsa za ta rika bawa mata N500 idan sun haihu a asibitocin gwamnati

Gwamnan Nigeria ya ce jiharsa za ta rika bawa mata N500 idan sun haihu a asibitocin gwamnati

  • Gwamna Ikpeazu na jihar Abia ya ce jiharsa za ta rika bawa kowacce mace da ta haihuwa a asibitin gwamnati tallafin N500
  • Gwamnan ya ce ko ba komai akwai mata talakawa da za su iya amfani da N500 su yi kudin mota idan za su koma gida bayan sun haihu
  • Ikpeazu ya ce bada N500 din yana cikin wani tsarin inshoran lafiya ne da gwamnatinsa ta bullo da shi ga mata masu karamin karfi

Gwamna Okezie Ikpeazu na jihar Abia ya ce jiharsa na bawa kowacce mace N500 idan ta zo ta haihu a cibiyoyin lafiya na bai daya a jihohin.

Gwamnan ya yi wannan jawabin ne a shirin Sunrise Daily na Channels TV a ranar Laraba.

Gwamnan Nigeria ya ce jiharsa za ta rika bawa mata N500 idan sun haihuwa a asibitocin gwamnati
Za mu rika bawa matan da suka haihuwa a asibitin gwamnati N500, In ji Ikpeazu
Asali: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kara karanta wannan

Bankin Afrika zai ba Gwamna Ganduje Dala miliyan 110 domin ayi ayyuka a kauyukan Kano

Mr Ikpeazu ya ce:

"Gwamnatin Abia ta shiga tsarin inshoran lafiya ga mata masu juna biyu. Idan kin haihu a kowanne cibiyoyin mu, za ki samu N500.
"Haihuwa kyauta ne, za a baki kayan haihuwa sannan a baki N500, ana hakan ne domin mutane masu karamin karfi a garuruwa."

Da aka masa tambaya kan ko mene N500 zai yi wa matan, gwamnan ya ce "haihuwa kyauta, kana tambayar talaka, me za ta yi da N500? Wasu daga cikinsu ba su da shi.' Ko kudin mota zuwa gida za su biya da shi."

A cewar tsarin lafiya bai daya na jihar Abia, akwai cibiyoyin lafiya bai daya 687 a kananan hukumomi 17 da ke jihar, Premium Times ta ruwaito.

Gwamnan ya ce sun bullo da tsarin haihuwa kyauta da bada N500 a matsayin inshoran lafiya don taimakawa mata masu juna biyu.

Yajin aikin likitoci

Likitoci na yajin aiki a jihar sakamakon rashin biyansu albashi na watanni 22.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: EFCC ta sanya gwamnan Anambra a jerin sunayen wadanda take nema

A watan da ta gabata, kwamitin asibitin koyarwa na jihar Abia, ABSUTH, ta rufe asibitin.

Kwallejin Fasawa wato Polytechnic ita ma ta tafi yajin aiki.

A cewar gwamnan, Kwallejin na jihar Abia da Asibitin Koyarwar hukumomi ne da aka kafa domin su rika samar da kudaden shiga amma suna fama da rashin jagoranci na gari.

Ya ce Kwallejin na iya daukan dalibai 15,000, wanda hakan zai iya bawa makarantar N3bn duk shekara, wanda za ta iya kula da kanta.

Mr Ikpeazu ya ce kudin da zai iya badawa kawai na bincike ne da gine-gine.

"Ba zan iya daukan nauyin biyan albashin hukumar da ya kamata tana samar da kudin shiga ba," a cewar sa.

Ana bin kowanne ɗan Najeriya bashin N64,684 bisa basukan da ƙasar ta ci a ƙasashen waje

A wani labarin, kun ji cewa bisa yawan ‘yan Najeriya da kuma yawan basukan da ake bin ta, kowa ya na da N64,684 a kan sa.

Kara karanta wannan

Jami'ar Soja ta gamu da cizon maciji cikin ban dakin gidanta dake barikin Soji, ta mutu

Kamar yadda kowa ya san yawan bashin da Najeriya take ta amsowa daga kasashen ketare, yanzu ko wanne dan Najeriya ya na da bashin $157 ko kuma N64,684 a kan sa.

Bisa wannan kiyasin, masanin tattalin arzikin kasa, Dr. Tayo Bello ya bayyana damuwar sa akai inda ya ce duk da zuzurutun basukan, babu wasu abubuwan ci gaba da aka samar wadanda za su taimaka wurin biyan basukan kamar yadda Leadership ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164

Tags: