Zamfara: 'Yan bindiga sun saka wa mutane haraji, sun ce wanda bai biya ba zai yaba wa aya zaƙin ta

Zamfara: 'Yan bindiga sun saka wa mutane haraji, sun ce wanda bai biya ba zai yaba wa aya zaƙin ta

  • Jama’an Magami da ke karamar hukumar Gusau a jihar Zamfara sun koka inda su ke bukatar taimako akan yadda rashin tsaro kullum ya ke kara tsananta a garuruwansu
  • Yanzu haka ‘yan bindiga sun sa musu haraji akan gonakinsu kuma matsawar mutum ya ki biya zasu banka wa amfanin gonan wuta su kurmushe
  • Duk da dai ‘yan sanda sun musanta wannan rahoton inda su ka ce babu wanda ya taba kai musu rahoto akan ‘yan bindiga sun lalata masa amfanin gona

Jihar Zamfara - Mutanen Magami da ke karamar hukumar Gusau a karkashin jihar sun koka yayin da su ke neman taimako akan yadda ‘yan bindiga su ka tasa su gaba, Vanguard ta ruwaito.

A cewarsu ‘yan bindiga suna ta lalata musu gonaki bayan kallafa mu su haraji da suke ta yi idan mutum ya ki biya sai su banka wa gonarsa wuta.

Kara karanta wannan

Sokoto: Sojoji sun yi lugude a kan 'yan bindiga, sun samo makamai da babura

Sai dai a wani rahoto na BBC Hausa, rundunar ‘yan sandan yankin sun musanta wannan labarin, sun ce babu wanda ya taba kai musu rahoto akan ‘yan bindiga sun lalata masa gona.

Ita ma NewsWireNGR ta ruwaito cewa wani mazaunin Magami a wata tattauna da manema labarai suka yi da shi ta wayar salula ya ce suna cikin babbar matsala.

Zamfara: 'Yan bindiga sun saka wa mutane haraji, sun ce wanda bai biya ba zai yaba wa aya zaƙinta
Yan bindigan Zamfara sun saka wa mutane haraji, sun yi barazanar hukunta wadanda ba su biya ba. Hoto: NewsWireNGR
Asali: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kamar yadda ya shaida:

“Kana barin Gusau kafin ka isa Magami, babban aiki ya sameka sai dai idan kana tare da jami’an tsaro.
“Tun da aka halaka MOPOL, a ranar su ka fara toshe hanyoyi, sun yi hakan ya kai sau 4 zuwa 5. Su na dakatar da manyan motoci su kwashe kaf kayan da ke cikinsu. Har haraji su ke amsa.
“Idan kuma ka isa Magami, za su dakatar da kai, ko dai su sace ka ko kuma su amshi haraji a hannunka.”

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun sace dan uwan hadimin Jonathan da wasu mutum 8 a Kwara

Ya ce sun banka wa gonaki biyu wuta

A cewarsa daga ranar Litinin zuwa yanzu, sun banka wa gonaki 2 wuta a Magami saboda ba su biya su haraji ba.

Ya kara da cewa manoman sun je gonarsu ne don kwaso amfanin gona ne, daga nan ‘yan bindiga su ka dakatar da su su ka banka wa gonar wuta saboda basu biya haraji ba.

A cewarsa sun sace mata 2 sannan sun kwace abin hawan manoman amma daga baya sun saki matan.

Ya ce sun bukaci kudi daga hannun manoman bai samu ba su ka banka wa gonar wuta kuma su ka yi barazanar ci gaba da kona gonar matsawar ba su biya su haraji ba.

Mutumin ya bayar da labarin yadda wasu ‘yan bindiga suka banka wa wasu wurare kusa da inda za a shiga garin Magami wuta kuma sai da suka kori jama’an garin tukunna suka kona garin.

Kara karanta wannan

Katsina: ‘Yan bindiga sun halaka jaruman ‘yan sanda 2 yayin musayar wuta

Har hanya suka toshe

Kuma a cewarsa sun toshe hanyar zuwa Magami don su nuna wa mutane cewa zasu ci gaba da cin karensu babu babbaka su na kona gonakin jama’a.

Ya bada bayanai akan yadda suke ikirarin ko dai mutum ya biyasu kudi, ko suyi garkuwa dashi su kuma banka wa gonarsa wuta.

“Kullum dai cikin matsala muke,” a cewarsa.

ISWAP na ƙokarin kafa daular ta a Jihar Neja, Gwamnatin jiha

A wani rahoton kun ji cewa gwamnatin jihar Neja ta koka akan yadda ISWAP take yunkurin kafa daularta a karamar hukumar Borgo da ke jihar, The Nation ta ruwaito.

Sakataren gwamnatin jihar Neja, Alhaji Ahmed Ibrahim Matane ya bayyana hakan ne yayin tattaunawa da manema labarai a Minna inda yace kungiyar ce ke da alhakin garkuwa da mutane a Dodo da ke Wawa.

The Nation ta bayyana yadda ya sanar da cewa kungiyar ISWAP tana shirin kafa daularta a wuraren babbar tashar Kainji da ke karamar hukumar Borgu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164