Labari mai dadi: Sanatoci sun nemi a karawa 'yan NYSC kudin alawus din abinci

Labari mai dadi: Sanatoci sun nemi a karawa 'yan NYSC kudin alawus din abinci

  • Majalisar dattawan Najeriya ta bayyana bukatar karin kudi kan kudin da ake ciyar da 'yan bautar kasa na NYSC
  • Wani sanata da ya tado da batun ya bayyana dalilai da suka janyo ya fara maganar, inda yace ya kamata ayi wani abu
  • Ya kuma bayyana cewa, ya kamata gwamnati ta duba kari kan kudaden da ke cikin kasafin kudin ma'aikatar harkokin matasa da wasanni

Abuja - Kwamitin majalisar dattawa mai kula da harkokin wasanni da ci gaban matasa ya bayar da shawarar karin kudin ciyar da 'yan NYSC a kullum daga Naira 600 ga kowane mutum zuwa N1,000, Punch ta ruwaito.

Shugaban kwamitin Obinna Ogba, ya yi wannan roko ne a ranar Talata yayin da yake gabatar da rahoton kwamitinsa kan kasafin kudin 2022 ga kwamitin kasafin kudi.

Kara karanta wannan

Ruwan kudi: Bidiyon yadda wasu mutane suke ta kwasar kudade a kan titi a Amurka

Majalisar dattawan Najeriya
Labari mai dadi: Sanatoci sun nemi a karawa 'yan NYSC kudin alawus din abinci | Hoto: punchng.com
Asali: UGC

Kwamitin majalisar dattawa mai kula da harkokin cikin gida a watan da ya gabata ya kara yawan alawus din ciyar da fursunonin da ke tsare a gidajen yari daga N450 zuwa Naira 1,000 a kowacce rana.

Ogba ya ce, abin takaici ne yadda ake ciyar da fursunonin sama da ‘yan NYSC da ke yi wa kasa hidima.

Jaridar Tribune Nigeria ta ruwaito shi yana cewa:

“Abin takaici ne yadda fursunonin da suka aikata laifuffuka ke morewa fiye da ’yan kungiyar matasa da ke yi wa kasa hidima.
“Bai kamata fursunonin su rika samun fiye da na matasan NYSC ba, domin alawus din ciyarwa ga ’yan NYSC shi ne Naira 600 ga kowane mutum a rana yayin da na fursunoni N1000 ne.

Kara karanta wannan

Kaduna za ta daina dogara da abin da za a samu daga asusun Tarayya - Gwamnatin El-Rufai

“Ni da kai za mu yarda cewa wannan ba daidai ba ne. Ina kira ne kawai ga bangaren zartarwa da majalisa da su yi wani abu a kan ’yan bautar kasa ta hanyar kara musu alawus na ciyar da su a kullum daga 600 zuwa Naira 1000 da kuma ingancin rigarsu.”

Dan majalisar ya kuma koka kan yadda kasafin kudin da aka ware wa ma’aikatar matasa da wasanni bai wadatar ba.

A cewarsa:

“Ya kamata a yi wani abu domin kasafin ba zai ishi ma’aikatar da matasa a ko’ina ba."

Sanata Smart Adeyemi ya kuma ce kara kudin ciyar da ‘yan NYSC din ya zama dole idan ana son su kasance masu kishin kasa.

Ya kara da cewa:

"Idan 'yan kungiyar ba su da isasshen abinci, zai yi wuya su kasance masu kishin kasa."

Hukumar NYSC ta koka kan kudin abinci: N650 ga 'yan NYSC, N1000 ga fursunoni

A wani labarin, hukumar NYSC ta koka kan yadda fursunonin da ke karkashin kulawar ma’aikatun hukumar gyaran jiki ta Najeriya ke samun na abinci fiye da na ‘yan NYSC.

Kara karanta wannan

Bidiyon budurwar da ta kashe N657k don yin karin gashi mai jan kasa ya janyo cece-kuce

Babban Darakta Janar na NYSC, Birgediya Janar Shuaibu Ibrahim, wanda ya bayyana haka a lokacin da ya bayyana a gaban wani kwamitin majalisa don kare kasafin kudi a ranar Larabar da ta gabata, ya ce ana ba 'yan NYSC abincin da ya kai na N217.

Don haka, ya bukaci Majalisar Wakilai da ta samar kari a kason abinci a kasafin kudin shirin na 2022.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.