Yanzu-yanzu: Zamu kara kudin mai, amma zamu fara baiwa yan Najeriya N5,000 kudin mota a wata: FG
- Biyo bayan rahoton Asusun Lamunin duniya, Gwamnatin tarayya tace zata cire tallafin mai a 2022
- Amma zamu fara baiwa yan Najeriya N5,000 kudin mota a wata, Ministar Kudi da kasafin kudin Najeriya
- Zainab Ahmad Shamsuna tace amma sai an cire tallafin za'a san adadin yan Najeriyan da zasu samu wannan kudi
Ministar kudi, kasafin kudi da shirye-shiryen kasa, Zainab Ahmad Shamsuna, ta bayyana cewa Gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari zata cire tallafin man fetur a 2022.
Idan Gwamnati ta cire wannan tallafi, kudin man fetur zai yi tashin gwauron zabo.
A madadin wannan tashi, Ministar kudin ta bayyana cewa Gwamnati za ta fara rabawa talakawan Najeriya dubu biyar-biyar a wata matsayin kudin mota.
Zainab ta bayyana hakan ne ranar Talata a taron kaddamar da rahoton Bankin Duniya (NDU), rahoton TheCable.
Labari da Hotuna: Yadda mata zasu iya taka rawar gani wajen tabbatar da zaman lafiya, Shugaba Buhari
A cewarta, talakawan dake Najeriya mutum guda milyan 30 zuwa 40 za'a rika baiwa wannan kudi wata-wata.
Tace amma sai an cire tallafin za'a san adadin yan Najeriya da zasu samu wannan kudi.
A jawabinta:
"Cigaba da biyan kudin tallafin man fetur ba zai yiwu ba. Gabanin shirin cire tallafin gaba daya nan da tsakiyar 2022, muna kokari tare da abokan aikinmu wajen rage zafi kan talakawa."
"Daya daga cikin hanyoyin rage zafin shine bada kudin mota na wata-wata N5000 ga mutane milyan 30 zuwa 40 da suka cancanta."
Nan da 2022 ku kara kudin lantarki da man fetur: Asusun Lamunin duniya ga Gwamnatin Najeriya
Asusun Lamunin duniya IMF a ranar Juma'a ya yi kira ga Gwamnatin Najeriya ta cire tallafin man fetur da na wutar Lantarki gaba daya a farko-farkon shekarar 2022.
Idan Gwamnati ta cire wannan tallafi, kudin man fetur da na lantarki zai tashi.
IMF ya bayyana hakan a jawabin da ta saki na ayyukan karshen 2021, inda ya ce cigaba da biyan kudin tallafi man fetur babban hadari ne rana goben tattalin arzikin Najeriya.
IMF ya jaddada cewa lallai a cire wannan tallafi kamar yadda aka tanada a dokar kamfanin man fetur PIA 2021.
Asali: Legit.ng