Bayan harin Lahadi, yan bindiga sun sake sace mutane ranar Litinin a titin Kaduna/Abuja
- Da alamun yan bindiga sun koma garkuwa da mutane hanyar Abuja-Kaduna bayan hutun dan lokaci
- Sau biyu kenan cikin kwana biyu da akayi awon gaba da dimbin matafiya a tsakiyar titi
- Gwamnatin jihar Kaduna har yanzu bata yi magana kan na wanda ya auku ranar Litinin ba
Abuja - Tsagerun yan bindiga masu garkuwa da mutane sun yi awon gaba da dimbin matafiya karo na biyu a babbar hanyar Kaduna zuwa Abuja ranar Lahadi, 22 ga Nuwamba, 2021.
Daily Nigerian ta ruwaito cewa yan bindigan sun farmaki matafiya ne misalin karfe 4:30 na yamma kuma suka budewa matafiyan wuta.
Masu idanuwan shaida sun bayyana cewa kusan waje daya aka tare matafiya ranar Litinin da Lahadi.
Mai idon shaida wanda ya tsallake rijiya da baya, Lawan Sani, yace akalla motoci hudu aka kwashe wadanda ke ciki.
Yace:
"Sojoji sun dira wajen da wuri amma tuni yan bindigan sun aikata aikinsu cikin mintuna sun shige daji da mutane."
"Na ga motoci 18-seater mallakin Zamfara Mass Transit, wata Toyota Yaris, Volkswajen Golf da kuma wata da ban san kirarta ba. An budewa motocin wuta."
Yunkurin ji daga Kakakin yan sandan Kaduna, Muhammad Jalige, ya ci tura.
Karo na biyu cikin mako guda
Haka ranar Lahadi muka kawo muku yadda yan bindiga sukayi awon gaba da matafiya a babban titin Kaduna zuwa Abuja.
Wani faifan bidiyo da aka saki a kafafen ra'ayi da sada zumunta ya nuna motoci akalla biyu da aka kwashe wadanda ke ciki tsakiyar titi.
A bidiyon na sakwanni 31, an ji mai daukan bidiyon yana cewa:
"Wayyo Allah, sun kwashe abokanmu, yanzu muke zuwa daga Kaduna. Yau 21 ga Nuwamba 2021."
Akalla mutum daya yan bindigan suka harbe har lahira.
Asali: Legit.ng