Budurwa ta gurfanar da tsohon saurayinta a gaban kotun musulunci saboda kai mata hari da dare

Budurwa ta gurfanar da tsohon saurayinta a gaban kotun musulunci saboda kai mata hari da dare

  • Sadiya Abubakar ta kai karar tsohon saurayinta gaban kotun musulunci saboda ya tare ta a kan hanya da daddare ya ci mata mutunci
  • A cewar matar yar kasuwa, tsohon saurayin ya mata haka ne saboda ta nemi ya biya bashin da take binsa na naira N100,000
  • Tsohon saurayin mai suna Hassan Mamoh ya bayyana cewa ba abinda ya mata illa kawai tafka mata mari a fuska

Kaduna - Wata budurwa yar kasuwa, Sadiya Abubakar, ranar Litinin, ta gurfanar da tsohon saurayinta Hassan Momoh, a gabam kotun musulunci dake zamanta a Magajin Gari, jihar Kaduna.

Dailytrust tace Sadiya ta ɗauki wannan matakin ne bisa harin da tsohon saurayin nata ya kai mata saboda ta nemi ya biya bashin da take binsa na N100,000.

Kara karanta wannan

'Yar Sarkin Kano Sanusi: Na gwammace ɓarawo ya sace kuɗin da in bawa miji na N500,000 ya ƙara aure

Kotun musulunci
Budurwa ta gurfanar da tsohon saurayinta a gaban kotun musulunci saboda kai mata hari da dare Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Mai gabatar da ƙara, Insp. Luka Sadau, ya shaida wa kotu cewa a ranar 11 ga watan Nuwamba aka kai rahoton lamarin caji ofis ɗin Magajin Gari.

Ya kara da cewa a watan Yuni, da misalin karfe 11:00 na dare, Sadiya ta rufe shagonta ta nufi gida, ba zato wanda ake zargin ya tare ta kan hanaya saboda ta nemi hakkinta na N100,000.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Shin tsohon saurayin ya amsa laifinsa?

Wanda ake zargin, Hassan Mamoh, da yake zaune a Anguwan Oriakpata, jihar Kaduna ya bayyana cewa abu ɗaya ya mata shine ya tafka mata mari.

Alkalin kotun, Mai shari'a Murtala Nasir, ya baiwa wanda ake kara beli a kan naira N100,000.

Hakanan kuma alkalin ya baiwa Mamoh sharaɗin beli na nemo wanda zai tsaya masa, kuma wanda ke da ɗaya daga cikin katin shaidar zama ɗan ƙasa.

Kara karanta wannan

Sheikh Pantami ya yi martani kan fastocinsa dake yawo na takarar shugaban kasa a 2023

Daga nan kuma sai mai shari'a Murtala Nasir, ya sanar da ɗage sauraron karar har zuwa 3 ga watan Disamba, a cewar hukumar dillancin labarai ta ƙasa (NAN).

A wani labarin na daban kuma Basarake ya gwangwaje diyarsa da kyautar mota bayan ta kammala digiri da daraja ta farko

Basaraken Oyo, Oba Lamidi Adeyemi III, ya nuna farin cikinsa da ni'imar da Allah ya yi wa diyarsa a karatunta.

Diyar Sarkin, Gimbiya Zainab Adebunmi Adeyemi, ta kammala karatun digiri da sakamako mafi girma, ta samu kyautar mota. Hotunan motar da suka watsu a kafafen sada zumunta ya jawo cece-kuce daga bakin mutane.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262