Innalillahi: Tsagerun yan bindiga sun harbe tsohon dan takarar gwamna a hanyar Abuja-Kaduna
- Miyagun yan bindiga sun harbe wani tsohon ɗan takarar gwamna a jihar Zamfara a kan hanyar Kaduna-Abuja
- Rahotanni sun tabbatar da cewa tsohon ɗan takaran, Alhaji Sagiru Hamidu, yana cikin matafiyan da harin yan bindiga ya rutsa da su
- Wani matafiyi da ya tsira daga harin, ya bayyana yadda suka ga motoci da yawa babu kowa a wurin da lamarin ya faru
Kaduna - Miyagun yan bindiga sun bindige wani tsohon ɗan takarar gwamnan jihar Zamfara dake arewa maso yammacin Najeriya, Alhaji Sagiru Hamidu, akan hanyar Kaduna-Abuja.
Aminiya Hausa ta rahoto cewa Alhaji Sagiru Hamidu na ɗaya daga cikin matafiyan da harin yan bindiga ya rutsa da su ranar Lahadi a babbar hanyan.
Rahotanni sun tabbatar da cewa miyagun yan bindigan sun harbi tsohon ɗan takarar ne yayin da suka bude wuta kan matafiyar da yammacin Lahadi.
Da Duminsa: Masu garkuwa sun kashe tsohon mai neman takarar gwamnan Zamfara a hanyar Abuja zuwa Kaduna
Lamarin dai ya faru ne a kusa da kauyen Rijana dake kan babbar hanyar ta Kaduna zuwa babban birnin tarayya.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Yadda lamarin ya faru
Daya daga cikin matafiyan da suka tsira, wanda ya bukaci a boye bayanansa, yace yan bindigan sun yi amfani da rashin kyaun hanyar, wanda yasa motoci ke tafiya a hankali kuma a hannu ɗaya.
Ya bayyana cewa maharan sun datse hanyar ne a kusa da kauyen Rijana da misalin karfe uku, kuma sun kwashe sama da awa ɗaya suna aikata mugun nufinsu ba tare da jami'an tsaro sun kawo ɗauki ba.
Ko taya suka kubuta daga harin?
A jawabinsa, mutumin yace:
"Da muka jiyo karar harbe-harbe a gabanmu, sai muka yo baya sosai, muka bada tazara mai nisa. Bayan wasu awanni sai mukaga motoci na wuto wa ta ɗaya hannun."
"Zata iya yuwu wa yan bindigan sun sace mutane da dama ko kuma tsoro ya sanya sun tsere cikin jeji saboda mun ga motoci akalla 15 ba kowa ciki yayin da muka wuce ta wurin da lamarin ya faru."
Har zuwa yanzun hukumar yan sanda reshen jihar Kaduna ba ta fitar da wata sanarwa dangane da harin ba.
A wani labarin na daban kuma Jirgin yakin sojoji ya yi ruwan bama-bamai kan sansanonin yan bindiga a Arewa, ya hallaka tsagerun da yawan gaske
Rahoto ya bayyana cewa manyan kusoshin yan bindiga da shugabannin su, sun mutu yayin harin a Sokoto, Zamfara.
A cewar wani jami'in soji, sabbin dabarun da dakarun sojin kasar nan suka fara amfani da shi ya fara haifar da ɗa mai ido.
Asali: Legit.ng