'Yan bindiga sun farmaki kwaleji, sun hallaka dalibi da wani lakcara a jihar Legas

'Yan bindiga sun farmaki kwaleji, sun hallaka dalibi da wani lakcara a jihar Legas

  • Wasu 'yan ta'aadda sun hallaka wani malamin a wani gari mai suna Poka a wani yankin jihar Legas
  • Hakazalika, majiyoyi sun bayyana yadda wani a harabar Kwalejin Ilimin Kiwon Lafiya ta Farko ta Michael Otedola (MOCPED)
  • An yi kira ga gwamnati da hukumomin tsaro da su dasa na'urorin tsaro a haranar kwalejin don magance matsalolin tsaro

Legas - An kashe wani malamin jami'a mai suna Ahmed Saheed da dalibin digiri dan aji daya a Kwalejin Ilimin Kiwon Lafiya ta Farko ta Michael Otedola (MOCPED) da ke karamar Hukumar Epe a Jihar Legas, Daily Trust ta ruwaito.

An ce an kashe malamin ne a kusa da garin Poka da ke Epe, yayin da dalibin mai suna Razak Bakare kuma aka harbe shi a harabar jami’ar.

Wata majiyar ‘yan sanda ta shaida wa Daily Trust cewa, lamurran masu ban takaici, sun faru ne cikin sa’o’i 48.

Kara karanta wannan

'Yan aware daga Kamaru sun shigo Najeriya, sun kashe mutane, sun kone gidaje

'Yan bindiga sun farmaki kwaleji, sun hallaka dalibi da wani lakcara a jihar Legas
Taswirar jihar Legas | Hoto: vanguardngr.com

‘Yan majalisa da sarakunan gargajiya na yankin ne suka tabbatar da rasuwar malamin da dalibin.

Sun ce yayin da aka bindige dalibin a ranar Laraba, an harbe malamin ne a ranar Juma’a.

A halin yanzu, akwai rashin kwanciyar hankali a harabar al'ummar Poka, a cewar Aladeshoyin na Odo-Noforija, a sashin Epe.

Oba Babatunde Ogunlaja, sarkin gargajiya na al’ummar, ya bayyana alhininsa kan faruwar lamarin.

Ya ce zaman lafiya a garin Noforija ya ruguje sakamakon kashe-kashen da aka yi.

Don haka ya yi kira ga mahukuntan cibiyar da su sanya na’urorin daukar hoto na CCTV a cikin harabar makarantar da kewayenta.

Ogunlaja ya kuma yi kira ga Gwamna Babajide Sanwo-Olu da kwamishinan ‘yan sanda, Hakeem Odumosu da su kara tura jami’an tsaro zuwa yankin.

Ya roki gwamnatin jihar Legas da ta sake gina katangar cibiyar da ta ruguje.

Kara karanta wannan

Yadda Buhari ya tattaro biliyoyin da aka sace, aka boye a Amurka, Ingila da Switzerland

Shi ma Sarkin Alara na masarautar Ilara, Oba Olufolarin Ogunsanwo, ya yi Allah wadai da faruwar lamarin, ya kuma bukaci jami’an tsaro da su kamo wadanda suka aikata wannan aika-aika.

Sai dai ya yi alkawarin cewa masarautar za ta tabbatar da cewa an dukufa wajen yakar irin wadannan munanan dabi’u a cikin al’umma.

An kame baburan 'yan achaba a Legas, an murkeshesu a bainar jama'a

Sakamakon karya dokokin hanya, sakateriyar Alausa da ke Ikeja, karkashin gwamnatin jihar Legas ta murkushe dimbin babura da aka kama a wurare daban-daban a Legas.

A watan Janairu, gwamnatin jihar ta haramta gudanar da ayyukan babura na kasuwanci - wanda aka fi sani da achaba - da babura masu kafa uku a kananan hukumomi 15, inji TheCable.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Hakeem Odumosu, ya halarci wurin da aka murkushe baburan akalla 482, inji rahoton The Sun.

'Yan kasuwa a Legas sun yi zanga-zangar nuna adawa da 'yar shugaban APC Tinubu

Kara karanta wannan

Albashi ba adadi: Abubuwa 6 da ya kamata ku sani game da limamin Harami, Sheikh Sudais

A wani labarin, daruruwan ‘yan kasuwa ne a babbar kasuwar Oyingbo a ranar Laraba suka gudanar da zanga-zangar nuna adawa da Misis Folashade Tinubu-Ojo, diyar shugaban jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Tinubu.

Tinubu-Ojo ita ce Iya Oloja Janar na Najeriya, PM News ta ruwaito.

An ce ta rufe kasuwar ne mako guda da ya gabata, saboda matsalar muhalli yayin da ta kulle dukkan harkokin kasuwanci.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.