Da dumi-dumi: Gwamnati ta haramta siyar da babura a wata jihar arewa

Da dumi-dumi: Gwamnati ta haramta siyar da babura a wata jihar arewa

  • Gwamna Abubakar Sani Bello na jihar Neja, ya haramta siyar da babura a cikin jihar
  • Gwamnatin ta Neja ta ce ta dauki wannan matakin ne sakamakon sabon salon da 'yan bindiga da masu garkuwa da mutane suka fito da shi na karbar babura a matsayin fansa
  • Babban sakataren gwamnatin jihar, Ahmed Ibrahim Matane, ne ya sanar da hakan a cikin wani jawabi a ranar Asabar

Jihar Neja - Wani rahoton jaridar Daily Trust ya nuna cewa gwamnatin jihar Neja ta haramta siyar da babura a cikin jihar.

Babban sakataren gwamnatin jihar, Ahmed Ibrahim Matane, wanda ya sanar da hakan a cikin wani jawabi a ranar Asabar, ya ce hukuncin ya biyo bayan matsalolin rashin tsaro da ake fama da su a wasu yankunan jihar.

Da dumi-dumi: Gwamnati ta haramta siyar da babura a wata jihar arewa
Da dumi-dumi: Gwamnati ta haramta siyar da babura a wata jihar arewa Hoto: The Governor of Niger-State
Asali: Facebook

Ya kuma ce an dauki matakin ne saboda bukatar da ‘yan bindiga da masu garkuwa da mutane ke gabatarwa na neman a basu babura a matsayin fansa.

Kara karanta wannan

Hankula sun tashi a jihar Nasarawa kan kisan wasu makiyaya

Sanarwar ta ce:

“Gwamnan jihar Neja, Alhaji Abubakar Sani Bello, ya yi umurnin haramta siyar da babura a fadin jihar.”

Matane ya ce baburan da haramcin ya shafa sun hada da Bajaj, Boxer, Qiujeng, Honda ACE, Jingchen da sauransu masu dauke da injin mai karfin 185cc.

Sakataren ya ci gaba da bayanin cewa gwamnatin jihar ta kara wannan matakin ne da nufin rage ayyukan miyagu a jihar.

Ya bayyana cewa gwamnatin ta yi watsi da hargitsin da yan bindiga da masu garkuwa da mutane ke haddasawa a wasu yankunan jihar sannan ta jadadda jajircewarta na fitar da jihar daga kowani irin barazana na tsaro.

Ya ce:

“Gwamnati na sane da rashin walwalar da matakin zai haddasawa mutane, amma an dauki matakin ne saboda ra’ayin jihar sannan ya roki dillalan babura a fadin jihar da su bayar da hadin kai a kan umurni.”

Kara karanta wannan

Gwamna Matawalle ya sake bude kasuwanni, ya ce lamarin tsaro ya inganta a Zamfara

Matane ya roki mutanen jihar da su ba hukumomin tsaro hadin kai a matakan tsaron da aka dauka domin kawo karshen ayyukan wasu miyagu, domin amfanin kowa, ruwayar Thisday.

Ya kuma bayyana cewa gwamnati ta umurci hukumomin tsaro a jihar da su tabbatar da an bi wannan umurni yadda ya kamata.

SSG din ya sake jadadda cewa har yanzu haramcin da aka sanyawa yan Kabu-kabu a garin Minna da kewaye na nan daram.

Hankula sun tashi a jihar Nasarawa kan kisan wasu makiyaya

A wani labarin, mun ji cewa an fara samun tashin hankali a Ashige, karamar hukumar Lafiya da ke jihar Nasarawa, sakamakon kashe wasu makiyaya biyu da wasu yan bindiga suka yi.

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa mummunan al’amarin ya afku ne a daren ranar Juma’a, 19 ga watan Nuwamba.

Rahoton ya kawo cewa an tsinci gawarwakin makiyayan ne a wani gona dauke da shaidar sara a fuskokinsu.

Kara karanta wannan

Rahoto: Yadda aka hallaka mutane 52 a Sokoto cikin kwanaki biyu kacal

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng