Nan da 2022 ku kara kudin lantarki da man fetur: Asusun Lamunin duniya ga Gwamnatin Najeriya
2 - tsawon mintuna
- Asusun Lamunin duniya ta yi kira ga Gwamnatin Najeriya da cewa nan da Junairun sabon shekara a cire tallafin mai da lantarki
- Idan Gwamnati ta cire wannan tallafi, kudin man fetur da na lantarki zai tashi kusan ninki biyu
- Yan Najeriya sun tofa albarkatun bakinsu kan wannan shawara da IMF ta baiwa gwamnatin Najeriya
Asusun Lamunin duniya IMF a ranar Juma'a ya yi kira ga Gwamnatin Najeriya ta cire tallafin man fetur da na wutar Lantarki gaba daya a farko-farkon shekarar 2022.
Idan Gwamnati ta cire wannan tallafi, kudin man fetur da na lantarki zai tashi.
IMF ya bayyana hakan a jawabin da ta saki na ayyukan karshen 2021, inda ya ce cigaba da biyan kudin tallafi man fetur babban hadari ne rana goben tattalin arzikin Najeriya.
Jawabin yace:
"A yanzu dai, rashin tabbas da ake cikin na bukatar a cire tallafin man fetur da wutan lantarki, a sauya yadda akae karban haraji, sannan a inganta lamarin canji."
"Cire tallafin mai da lantarki gaba daya abune da ya kamata ayi da gaggawa, sannan kuma a taimakawa talakawa da wani abu na rage zafi."
IMF ya jaddada cewa lallai a cire wannan tallafi kamar yadda aka tanada a dokar kamfanin man fetur PIA 2021.
A cire tallafin wutan lantarki
IMF ya cigaba da cewa cire tallafin wutan lantarki shime ayi da gaggawa nan zuwa Junairun 2022 kuma kada ayi jinkiri.
Yace:
"Akwia bukatar baiwa mutane taimako domin rage zafin wannan abu kan talakawa, musamman yanzu da abubuwa ke hauhawa."
Asali: Legit.ng