Budurwar da aka yiwa sharrin safarar kwayoyi a kasar Saudiyya ta zama jami’ar NDLEA

Budurwar da aka yiwa sharrin safarar kwayoyi a kasar Saudiyya ta zama jami’ar NDLEA

  • Budurwar da aka yiwa sharri a kasar Saudiyya kan safarar kwayoyi ta zama jami’ar NDLEA a Najeriya
  • Zainab na cikin daliban da aka yaye a makarantar NDLEA ranar Juma'a a bikin da ya gudana a garin Jos
  • Yan Najeriya da dama sun tofa albarkatun bakinsu kan wannan abu

Budurwa yar jihar Jigawa, Zainab Aliyu Kila wacce aka yiwa sharrin safarar kwayoyi yayinda ta tafi aikin Umrah kasar Saudiyya ta shiga hukumar yaki da kwayoyin Najeriya NDLEA.

Zaku tuna cewa a shekarar 2018, Gwamnatin Saudiyya ta daure Zainab Aliyu Kila a Kurkuku kuma ana shirin yanke mata hukunci.

Daily Nigerian ta ruwaito cewa Zainab na cikin sabbin Jami'ai 2000 da hukumar NDLEA ta yaye a makarantarta dake Jos, jihar Plateau ranar Juma'a.

Jaridar tace mahaifin Zainab, Habibu Kila ya tabbatar da hakan inda yace lallai tana da mukamin ASN yanzu.

Kara karanta wannan

Bukatar sakin Nnamdi Kanu babban lamari ne, amma zan yi shawara: Buhari ga Dattawan Igbo

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Budurwar da aka yiwa sharrin safarar kwayoyi a kasar Saudiyya ta zama jami’ar NDLEA
Budurwar da aka yiwa sharrin safarar kwayoyi a kasar Saudiyya ta zama jami’ar NDLEA Hoto:Daily Nigerian
Asali: Facebook

Zamana a gidan yari – Zainab Aliyu

Zainab Aliyu mai shekaru 22 da haihuwa ta tsinci kanta cikin wani maiwuyacin hali inda aka kama jakarta da miyagun kwayoyi a kasa mai tsarki.

Hukuncin wannan laifi kuwa shine kisa a bisa dokokin kasar ta Saudiya. Bayan an dauki tsawon lokaci anata kai ruwa rana yayin bincike da kuma tattaunawa tsakanin kasashen Najeriya da Saudiya, an samun gano gaskiyar lamarin cewa ba ita keda mallakar kwayoyin ba cusa mata akayi cikin jakarta ba tareda sanin ta ba.

Karanta yadda tayi zaman gidan yarin kamar yadda ta shaidawa jaridar Daily Trust a nan: https://hausa.legit.ng/1239006-zamana-a-gidan-yari-zainab-aliyu.html

Bayan kubuta daga gidan yarin Saudiyya, Zainab Aliyu ta kammala NYSC

Zainab Aliyu, ta kammala hidimar kasarta bayan kimanin shekaru biyu da kubuta daga gidan yari.

Kara karanta wannan

Barazanar sabon yajin aiki: Kakakin Majalisa ya shiga tsakanin ASUU da Gwamnatin tarayya

Abike Dabiri-Erewa ce ta wallafa hakan a shafinta na Twitter tare da hoton matashiyar.

Kamar yadda ta wallafa,

"Kun tuna Zainab Aliyu, wacce aka garkame babu laifinta a kasar Saudi Arabia sakamakon ganin miyagun kwayoyin da aka yi a cikin kayanta? A yau ta kammala hidimar kasa. Muna mata fatan alheri tare da nasara a rayuwarta."

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng