Bayan kubuta daga gidan yarin Saudiyya, Zainab Aliyu ta kammala NYSC
Zainab Aliyu, matashiya 'yar Najeriya da aka saka wa miyagu kwayoyi a cikin kayanta ba tare da saninta ba, wacce shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kai wa dauki, ta kammala hidimar kasarta.
Abike Dabiri-Erewa ce ta wallafa hakan a shafinta na Twitter tare da hoton matashiyar.
Kamar yadda ta wallafa, "Kun tuna Zainab Aliyu, wacce aka garkame babu laifinta a kasar Saudi Arabia sakamakon ganin miyagun kwayoyin da aka yi a cikin kayanta? A yau ta kammala hidimar kasa. Muna mata fatan alheri tare da nasara a rayuwarta."
Idan za ku tuna tattaunawar da aka yi da Zainab Aliyu bayan sakinta, ta ce ta koyi larabci tare da haddace rabin Al-Qur'ani mai girma a zaman kwanaki 124 da tayi a gidan yari.
An kama Zainab a ranar 26 ga watan Disamba bayan ganin Tramadol, wani magani da aka shiga da shi kasar Saudiyya a jakarta.
Zaina wacce ta kasance dalibar jami'ar Maitama Sule da ke Kano a waccan lokacin, ta je kasar Saudiyya ne don yin Umra tare da mahaifiyarta da 'yar uwarta.
A wata tattaunawa da tayi da Daily Trust, ta bayyana abinda ta fuskanta a yayin da take tsare.
Yadda ta daina yarda da mutane da kuma yadda tayi kawance da wata budurwa 'yar kasar Ethiopia mai suna Rehisty.
KU KARANTA KUMA: Yanzu-yanzu: 'Yan sanda sun zagaye gidan tsohuwar MD ta NDDC
"Na hadu da mutane da yawa. Amma ina tabbatar muku da cewa na dauki kwanaki masu tarin yawa kafin in fara yarda da mutane.
"Tunda na gane sharri aka yi min, na daina yarda da mutane. Bana yarda da jama'a har da mazauna gidan gyaran halin," Aliyu tace.
"Na koyi larabci. Na shiga hadfa kuma na haddace rabin Qur'ani mai girma a zaman a gidan yarin. Na koya yadda zan zauna da mutane daga wurare daban-daban."
A yayin bayanin yadda aka dauketa daga dakin otal dinta zuwa lokacin da ka saketa, Aliyu ta ce sai da ta shade kusan mako daya kafin ta yadda cewa gidan yari take.
Ta ce ana matukar kula da su domin basu fuskantar tsangwama ko cin zarafi.
"Na kwashe kusan sati ban san a gidan yari nake ba, saboda ban san wani laifi da nayi ba," tace.
Aliyu ta yi godiya ga gwamnatin tarayya da kowa wanda yayi kokarin ganin fitowarta.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng