Zamana a gidan yari –Zainab Aliyu

Zamana a gidan yari –Zainab Aliyu

Zainab Aliyu mai shekaru 22 da haihuwa ta tsinci kanta cikin wani maiwuyacin hali inda aka kama jakarta da miyagun kwayoyi a kasa mai tsarki. Hukuncin wannan laifi kuwa shine kisa a bisa dokokin kasar ta Saudiya.

Bayan an dauki tsawon lokaci anata kai ruwa rana yayin bincike da kuma tattaunawa tsakanin kasashen Najeriya da Saudiya, an samun gano gaskiyar lamarin cewa ba ita keda mallakar kwayoyin ba cusa mata akayi cikin jakarta ba tareda sanin ta ba.

Zamana a gidan yari –Zainab Aliyu
Zamana a gidan yari –Zainab Aliyu
Asali: Facebook

KU KARANTA:Yan sandan Binuwe sun kama mutum 30 cikin mako guda

A ranar Litinin ta dawo gida Najeriya bayan ta kwashi tsawon watanni hudu a gidan kaso. Ga kadan daga cikin yadda tayi zaman gidan yarin kamar yadda ta shaidawa jaridar Daily Trust:

Jaridar Daily Trust: Shin ko za ki iya fada mana halin da kika tsinci kanki a gidan yarin Saudiya tsawon watanni hudu?

Zainab Aliyu: Mun kasance muna bacci nida mahaifiyata da yar uwata Hajara a dakin otal din muka sauka, kwatsam sai wasu jami’an tsaro larabawa tareda bakaken fata biyu sun fado mana. Suka tashe mu daga bacci suna tambayarmu akan jakar da muka baro dauke da kwayoyi a tashar jirgin saman Jiddah. Nan muka fada masu bamu da masaniya akan jakar da suke magana akai, sai suka sanar da mahaifiyata cewa zan bisu zuwa ofishinsu saboda jakar me dauke da kauyoyin sunana take dauke dashi.

Daily Trust: Akwai wanda ya sanar dake cewa za’a kai ki gidan yari?

Zainab: A’a babu wanda ya sanar dani. Ko bayan an kai ni can ma banyi tsammanin cewa gidan yari bane. Saboda ni har a raina nasan cewa ban aikata laifin komi ba. Daga baya na lura cewa tabbas gidan yari aka kawo ni. Nan suka bani daki, mu hudu ne a dakin a ciki na samu aron wayar salula na kira mahaifiyata.

Daily Trust: Kin kuwa yi abokai a gidan yarin?

Zainab: Eh nayi abokiya guda daya, yar kasar Habasha. Mun dade bamu magana saboda ita turanci kadan take ji ni kuma larabci kadan nakeji. Amma daga baya na iya larabci kwarai da gaske saboda haka muka fara magana da ita. Mun shaku da juna sosai kasancewar rana daya aka kawo ni da ita.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

KU LATSA : Domin karuwa cikin wannan wata mai albarka na Ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel