'Yan ta'adda sun kashe sojoji 337 a Nigeria cikin shekaru 2, Rahoto
- Rahoton cibiyar bincike ta SBM intelligence ya fitar ya nuna cewa yan ta'adda sun halaka sojoji 337 daga 2019 zuwa yanzu
- Rahoton ya kuma ce an kashe yan ta'adda 92 da wasu mutane 111 da ba a bayyana ko su wanene ba
- Har ila yau, rahoton ya nuna cewa jihar Borno ne aka fi kai hare-haren sai, Zamfara, Yobe, Kaduna, Katsina, Kebbi, Sokoto
Wani rahoto da cibiyar bincike ta SB Morgan (SBM) intelligence ta fitar a ranar Alhamis ya nuna cewa yan ta'adda sun kashe mutane 569, ciki har da sojoji 337 a hare-hare tun shekarar 2019, The Cable ta ruwaito.
Cibiyar ta SMB Intelligence, mai gudanar da bincike, ta dade tana tattara bayanai da alkalluma kan abubuwan da ke faruwa a Nigeria.
Rahoton ya kuma ce an kashe jami'an yan sandan Nigeria 29 da Yan sa kai a wa'addin na shekaru biyu.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
A cewar rahoton, an kashe 'yan ta'adda 92 da wasu mutane 111 da ba a bayyana ko su wanene ba a yayin hare-haren da aka kai.
Daily Trust ta ruwaito cewa rahoton ya nuna cewa yankin arewa maso gabas aka fi kai hare-hare, 53, sai kuma arewa maso yamma, tara.
Jihohin da aka fi kai hari
Borno - 45
Zamfara - 7
Yobe - 4
Kaduna - 2
Katsina - 2
Kebbi - 1
Sokoto - 1
A ranar Asabar, mayakan ISWAP sun kashe Dzarma Zirkusu, Birgediya Janar da wasu sojoji guda uku.
An kai wa Janar din farkmaki ne yayin wani harin kwanton bauna da aka kai masa yayin da ya ke hanyarsa na zuwa Askira don kaiwa sojojin da ke yankin dauki.
Harin na daya daga cikin hare-haren da 'yan ta'addan suka kai wa sojojin Nigeria.
Rahoto: Masu ƙera wa Boko Haram bama-bamai sun koma dazukan Kudancin Kaduna
A jiya, kun ji cewa shugabannin kungiyar Boko Haram da ke biyayya ga Bakoura Buduma sun mayar da masu hada musu bama-bamai dazukan yankin kudanci Kaduna, a cewar wani rahoton da PRNigeria ta fitar.
A baya-bayan nan ne aka mayar da masu hada bama-baman da ake kira Amaliyyah a tsakin 'yan ta'addan, zuwa Rijana, Igabi da Chikun a yankin kudancin Kaduna.
Majiyoyi daga ciki sun ce kungiyoyin biyu na Boko Haram za su yi amfani da duwatsun da ke yankin a matsayin mabuya.
Asali: Legit.ng