Zargin damfarar N2bn: EFCC ta garkame kadarorin tsohon daraktan sojin ruwa

Zargin damfarar N2bn: EFCC ta garkame kadarorin tsohon daraktan sojin ruwa

  • Hukumar EFCC ta rufe wasu kadarorin tsohon darektan asusai na sojojin ruwan Najeriya, Rear Admiral Tahir Yusuf (Rtd)
  • An samu bayanai akan yadda ya ke da kadarori a Zaria da Kaduna wadanda aka garkame a kwanakin karshen mako da ranar Laraba
  • Hakan ya biyo bayan zarginsa da almundahana tare da wawurar kudade har naira biliyan 2 da gwamnati ta ke yi masa

Hukumar yaki da rashawa ta EFCC ta garkame wasu kadarorin da tsohon darektan asusai na sojin ruwan Najeriya, Rear Admiral Tahir Yusuf (Rtd) ya mallaka.

Daily Trust ta ruwaito yadda ya ke da kadarori a Zaria da Kaduna wadanda aka garkamesu tun kwanakin karshen mako wasu kuma ranar Laraba bisa zarginsa da almundahanar N2bn.

Kara karanta wannan

Kano: Alƙalin Kotun Shari’ar Musulunci Ya Aike da Alhassan Yusuf Gidan Ɗan Kande Saboda Satar Kare

Zargin damfarar N2bn: EFCC ta garkame kadarorin tsohon daraktan sojin ruwa
Zargin damfarar N2bn: EFCC ta garkame kadarorin tsohon daraktan sojin ruwa. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

Majiyoyi sun nuna yadda ya ke da kadarori kamar su Otal din Emerald da ke Zaria, wasu gine-gine 2 da ba a kammala ba a Zaria da Kaduna da kuma gidan buredin Bitmas da ke Zaria.

“Eh, tabbas an garkame kadarorinsa. Sakamakon karon battar da su ke yi da EFCC,” kamar yadda wata majiya ta shaida Daily Trust.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Dama tun kafin yanzu EFCC ta ke cigiyarsa inda daga bisani ya lallaba ya shigo Najeriya ta kasar Nijar.

Ya bar Najeriya zuwa Dubai, UAE, a 2018 bayan an zarge shi da satar N2bn wadanda kudi ne na sojin ruwan Najeriya inda ya yi aiki.

Babbar kotun tarayya da ke zama a Abuja a 2020, ta umarci kwace N500m da ake zargin Yusuf ya wawura tare da zuba su a asusun gwamnatin tarayya.

Kara karanta wannan

Yajin aikin ASUU: FG za ta rabawa jami’o’i biliyan N22.72 a ranar Laraba – Ministan Buhari

Bisa umarnin alkali Ijeoma Ojukwu, Yusuf zai mayar da N392,695,857.87 da $91,955.38 da £15,050 da ke cikin asusunsa na gida.

Kakakin EFCC ya sanar da Daily Trust cewa, bai samu wani bayanai ba akan abinda ke wakana a halin yanzu.

“Bani da wani labari dangane da batun,” kamar yadda ya ce.

Labarin rigar mama ta lu'u-lu'u a kayan Diezani: Shugaban EFCC ya yi karin haske

A wani labari na daban, Abdulrasheed Bawa, shugaban hukumar yaki da rashawa tare da hana yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa, EFCC, ya ce babu wasu rigunan mama da aka samo daga Diezani Alison-Madueke, tsohuwar ministar man fetur, TheCable ta wallafa.

Diezani, wacce ta hanzarta barin kasar nan bayan tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ya mika mulki ga shugaban kasa Muhammadu Buhari a 2015, an zarge ta da sace $2.5 biliyan daga gwamnatin tarayya yayin da ta ke minista, lamarin da ta musanta.

Kara karanta wannan

Rahoton EndSARS: HURIWA ta bukaci Buhari ya fatattaki Lai Mohammed kan karyar da ya zuga

Tuni hukumar EFCC ke kokarin dawo da ita kasar Najeriya, A watan Oktoba, gwamnatin tarayya ta jero wasu kadarori da ta kwace daga Diezani wanda suka hada da tamfatsesen gida a Banana Island Foreshore Estate, Ikoyi, Lagos.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng