Farashin litan man fetur zai iya tashi N170, Yan kasuwar mai
- Yan kasuwar mai sun bayyana matakin da zasu dauka nan da kwanaki masu zuwa kan farashin mai
- A makon nan, an fara fuskantar matsalar tsada da karancin man fetur a birnin tarayya da wasu jihohi
- Kamfanin NNPC tace yan Najeriya su kwantar da hankulansu akwai isasshen man a ajiye
Da yiwuwan farashin litan man fetur ya tashi daga N165 zuwa N175 yayinda farashin ex-depot zai tashi daga N159 zuwa N165, yan kasuwar mai sun bayyana ranar Alhamis.
Jaridar Punch ta ruwaito cewa kungiyar yan kasuwan mai masu zaman kansu IPMAN da kuma kungiyar dillalan mai a Najeriya PETROAN sun yi gargadin hakan muddin ba'a dau mataki ba.
Yan kasuwan sun yi korafin karancin mai wanda hakan ya tilastawa masu ajiyar mai kara farashin lita daga N148 zuwa N159
Ku sani mambobin IPMAN da PETROAN ne mammalakan mafi akasarin gidajen mai a Najeriya.
Yan kasuwan sun yi bayanin cewa wannan abu na faruwa ne saboda gwamnatin tarayya ta ki dabbaka yarjejeniyar da akayi tsakanin masu ruwa da tsaki.
A makon da ya gabata, NNPC ta amince da daina amfani da Dalar Amurka wajen cinikayyar tafiyar da mai, amma har yanzu ba'a daina ba.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Masu ajiyar mai kuwa (ex-depot) sun ce biyan da sukeyi a Dala shine babban dalilin tsaiko wajen rabon man kuma hakan ya haddasa karanci.
Ko shakka babu farashin litan mai zai tashi
Kakakin kungiyar IPMAN, Chief Ukadike Chinedu, yace ko shakka babu farashin litan mai zai tashi muddin farashin ex-depot bai sauko ba.
Yace,
"Tabbas (zai tashi), saboda idan ya duba riban da ake samu, za ka lura cewa an takaita."
"Ita kuma gwamnati na maganan janye tallafi. Ba zaku iya janye tallafi kuma ku rika fada mana farashin da zamu sayar ba."
"Saboda haka daga yanzu, yan kasuwa zasu tada farashin daga N165 zuwa N170."
Shugaban kungiyar dillalan mai PETROAN, Billy Gillis-Harry, ya tabbatar da matsayar IPMAN inda yace ba da dadewa ba dillalai a gidajen mai zasu kara farashi muddin farashin ex-depot bai sauko ba.
Ku kwantar da hankulanku, ba za'a yi wahalan mai ba - Mele Kyari ga yan Najeriya
Kamfanin Man Feturin Najeriya, NNPC, ta kwantarwa da yan Najeriya hankali game da rade-radin tsadar mai yayinda aka fara fuskantar karanci a wasu jihohin Najeriya.
Dirakta Manaja na NNPC, Mele Kyari, ya bayyanawa yan Najeriya cewa su kwantar da hankulansu akwai isasshen man da zai isa ba tare da an sha wahala ba.
Kyari ya bayyana hakan ne a jawabin da yayi a taron manema labaran sashen makamashi na Najeriya NAEC2021, ranar Talata a jihar Legas, rahoton NAN.
Asali: Legit.ng