Yanzu-yanzu: Gagarumar gobarar gas ta hargitsa garin Ibadan

Yanzu-yanzu: Gagarumar gobarar gas ta hargitsa garin Ibadan

  • Mummunar gobarar gas ta tashi a garin Ibadan inda ta tarwatsa titin da ke da kusanci da UCH a Ibadan
  • Kamar yadda bidiyon ya nuna, an ga manyan gine-gine suna ci da wuta a yankin da lamarin ya auku
  • An bukaci masu ababen hawa da ke bin hanyar da daren yau da su sauya hanya domin gobarar ta tashi wurin karfe 9

Ibadan, Oyo - Gagarumar gobarar ta tashi a kusa da NTA inda titin da ke kusa da yankin UCH ya tarwatse a garin Ibadan da ke jihar Legas.

The Nation ta gano cewa, mummunar gobarar ta tashi ne wurin karfe 9 na dare. A bidiyon da The Nation ta gani, gine-gine masu tarin yawa sun tashi da gobarar.

Read also

Kano: Motar Giya Ta Faɗi Kusa Da Ofishin Hisbah, Wasu Sun Ƙi Kai Dauƙi Don Gudun Fushin Allah

Da duminsa: Gagarumar gobarar gas ta hargitsa garin Ibadan
Da duminsa: Gagarumar gobarar gas ta hargitsa garin Ibadan
Source: Original
Kamar yadda aka ce: "Mummunar gobarar gas din ta tashi wurin NTA inda ta fashe titin da ke kafin UCH, Ibadan. Ana roko duk wanda ke tuki ta wurin a wannan daren da ya sauya hanya."

Har zuwa lokacin rubuta wannan rahoton, ba a san yawan wadanda suka rasa rayukansu ba.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel