Sauyin yanayi: Shugaba Buhari ya rattaba hannu kan wasu sabbin dokoki guda biyu
- Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya rattaba hannu kan wasu dokoki guda biyu da suka shafi sauyin yanayi
- Shugaban ya rattaba hannun bayan da majalisun kasar suka amince da kudurorin bayan tsallake karatu na uku
- Sanarwar rattaba hannun ta fito ne daga hannun Garba Shehu, hadimin Buhari a harkokin yada labarai
Abuja - Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sanya hannu kan dokar sauyin yanayi ta zama doka a Najeriya.
Labarin sanya hannun na fitowa ne daga Garba Shehu, babban mataimaki na musamman ga shugaban kasa kan harkokin yada labarai da yada labarai, a yau ranar Alhamis.
Idan baku manta ba, majalisar wakilai da ta dattawa ta amince da kudurin dokar sauyin yanayi bayan ta zarce karatu na biyu da na uku.
A cikin sanarwar da Garba Shehu ya fitar ta shafin Facebook, ya ce:
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
"Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya rattaba hannu kan wasu muhimman kudirori guda biyu da majalisar dokokin kasar ta amince da su wanda hakan ya sanya su zama wani bangare na dokokin tarayya.
"Dokar sauyin yanayi ta samo asali ne daga wani kudurin doka da dan majalisar wakilai, Sam Onuigbo ya dauki nauyinta, ta kuma tanadi wasu abubuwa da suka shafi sauyin yanayi da kuma kafa majalisar kasa kan sauyin yanayi.
"Har ila yau, tana ba da hanyar yin lissafin muhalli da tattalin arziki da kuma yunkurin samar da tsarin karshe na fitar da kasa daga kangin sauyin yanayi."
Hakazalika, Buhari ya rattaba hannu kan kwaswarima ga dokar AMCIN mai lamba 4, 2010.
A cewar sanarwar:
"Dokar Hukumar Kula da Kadarori ta Najeriya ta yi wa dokar AMCON kwaskwarima mai lamba 4, 2010."
Babu wanda ya cancanci a yi murnar ranar haihuwarsa kamar Mamman Daura, inji Buhari
A wani labarin, shugaban kasar Najeriya, Manjo Muhammadu Buhari mai ritaya ya taya Malam Mamman Daura murnar maulidinsa na cika shekaru 82 a duniya.
Shugaban, a wata sanarwa da ya fitar ta shafin Facebook ranar Laraba dauke da sa hannun hadiminsa kan harkokin yada labarai, Garba Shehu, ya yi murnar maulidin dan uwa kuma makusancin nasa.
Buhari ya ce babu wanda ya cancanci a taya murnar maulidi kamar Malam Daura.
Asali: Legit.ng