Sakataren harkokin wajen Amurka ya gana da Buhari a Aso Rock Villa
- Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gana da sakataren harkokin wajen kasar Amurka a fadarsa ta Villa
- Shugaban ya gana da Antony Blinken ne da yammacin yau Alhamis 18 ga watan Nuwamba, shekarar 2021
- Hakazalika, sakataren na harkokin wajen kasar Amurka zai kuma gana da mataimakin shugaban kasa, Osinbajo
Abuja - The Nation ta ruwaito cewa, Sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken na ganawa da shugaban kasa Muhammadu Buhari a fadar shugaban kasa dake Abuja.
Blinken ya isa fadar Aso Rock Villa ne da misalin karfe 3:47 na rana, kuma babban jami’in hulda da jama’a na kasa (SCOP), Ambasada Lawal Kazaure, wanda ya kai shi ofishin shugaban kasar ne ya tarbe shi.
Bayan ganawar da Buhari, sakataren harkokin wajen kasar ta Amurka zai zarce zuwa ofishin mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo inda zasu rattaba hannu kan wasu yarjejeniyoyin Najeriya da kasar Amurka.
Bayan haka kuma zai yi taron manema labarai na hadin gwiwa tare da Ministan Harkokin Waje, Geoffrey Onyeama, kafin ya bar fadar shugaban kasa.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
A wasu hotuna da Legit.ng Hausa ta samo daga shafin Facebook na hadimin Buhari kan harkokin yada labarai na zamani, Buhari Sallau, an ga lokacin da shugaba Buhari ya karbi jami'in na Amurka.
Kalli hotunan:
Shugaba Buhari ya rattaba hannu kan wasu sabbin dokoki guda biyu
A wani labarin, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sanya hannu kan dokar sauyin yanayi ta zama doka a Najeriya.
Labarin sanya hannun na fitowa ne daga Garba Shehu, babban mataimaki na musamman ga shugaban kasa kan harkokin yada labarai da yada labarai, a yau ranar Alhamis.
Idan baku manta ba, majalisar wakilai da ta dattawa ta amince da kudurin dokar sauyin yanayi bayan ta zarce karatu na biyu da na uku.
Asali: Legit.ng