Rikici ya kunno kai tsakanin El-Rufai da malaman makaranta kan batun jarrabawar kwarewa

Rikici ya kunno kai tsakanin El-Rufai da malaman makaranta kan batun jarrabawar kwarewa

  • Gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ya sanyawa daukacin malaman makarantun firamare yin jarabawar kwarewa kan karantarwar a jihar
  • A cikin watan Disamba ne gwamnatin jihar Kaduna ta shirya gudanar da jarabawar domin tantance kwarewar malamai a jihar.
  • Sai dai kungiyar malamai ta kasa ta ce mambobinta da su yi watsi da batun jarabawar kwarewa da gwamnan ya shirya

Malamai a jihar Kaduna da gwamnan jihar, Nasir El-Rufai, na ci gaba da fafatawa a kan batun jarrabawar kwarewa da gwamnatin jihar ke shirin yi.

Gwamna El-Rufa’i ya shirya yi wa malaman Kaduna jarabawar tantance kwarewarsu a matsayin da suke na karantarwa a jihar.

El-Rufai, Malaman Kaduna sun jagoranci zanga-zanga kan Jarrabawar kwarewa
Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai | Hoto: dailytrust.com
Asali: Facebook

PM News ta ruwaito cewa gwamnatin jihar ta tsara gudanar da jarabawar kwarewar malaman makarantun firamare a watan Disamba 2021.

NUT ta bayyana matsayinta akan jarabawar kwarewa ga malamai

Kara karanta wannan

Babu unguwar da babu yan kwaya a Najeriya, Janar Buba Marwa

Sai dai Majalisar zartaswar kungiyar Malaman Najeriya (NUT) ta yi kira ga mambobin kungiyar da su yi watsi da batun jarabawar.

Kelvin Nwankwo, shugaban kungiyar na kasa ya shawarci mambobinsu da ke makarantun firamare a jihar da kada su zana jarrabawar da gwamnan jihar ya shirya.

Ya kuma ce hukumar zartaswar kungiyar ce ke da ta cewa a matakin da reshen jihar Kaduna ya dauka kan lamarin.

Nwankwo ya bayyana cewa tuni jami’o’i da kwalejojin ilimi daban-daban da aka amince da su a fadin kasar nan suka tabbatar da kwarewar malaman kafin a dauki dukkansu aiki.

Bugu da kari, jaridar Punch ta ruwaito cewa NUT ta kuma bayyana cewa, dokar kasa ta 1(d) ta kungiyar rijistar malamai ta Najeriya (TRCN) wato CAP.T3 LFN 2004, ta riga ta yi tanadin tsari da sarrafa aikin koyarwa.

Kara karanta wannan

Ana wata ga wata: Gwamnatin Buhari za ta yi aikin canza taswirar Najeriya

Nwankwo ya ce malamai a duk fadin Najeriya suna nan suna shirye don shiga kwasa-kwasai da karatuttuka da horaswa wadanda za su iya cike gibin ilimi a fannonin da suka kware.

Ya kara da cewa:

"Duk da haka, muna adawa da duk wata dabara ta siyasa da nufin rage malamai a fagen aiki, tare da fakewa da cewa wadannan malaman sun fadi jarabawa."

Yajin aiki: FG ta gargadi kungiyoyin kwadago ma'aikata kan amfani da kungiya ana karya doka

A wani labarin, Gwamnatin tarayya ta ce za ta dauki cikakken matakin doka a kan wadanda ke ci gaba da tsallake layi a cikin rigar kungiyanci ta ma'aikata.

Ministan kwadago da samar da ayyukan yi, Sen. Chris Ngige ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da Mista Charles Akpan, mataimakin daraktan yada labarai da hulda da jama’a na ma’aikatar ya fitar ranar Talata a Abuja, Vanguard ta ruwaito.

Ma’aikatan ma’aikatar ciniki da zuba hannun jari sun rufe kofar shiga ma’aikatar a ranar Larabar da ta gabata a yayin wata zanga-zangar neman a tsige sakatariyar dindindin, Evelyn Ngige, wadda ita ce uwargidan ministan kwadago da samar da ayyukan yi, Chris Ngige.

Kara karanta wannan

Yadda aka yi ruwan sama a Masar, kunamai sun addabi mutane a cikin gidajensu

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.