Da Dumi-Dumi: DPO na yan sanda ya lashe gasar karatun Alkur'ani Izu 60 a jihar Kano
- A karon farko, kwamishinan yan sandan jihar Kano, Sama'ila Dikko, ya shirya musabakar Alkur'ani tsakanin dakarun yan sanda
- Mahaddatan jami'an yan sanda a mataki daban-daban sun fafata yayin musabakar, daga karshe aka bayyana waɗan da sukayi nasara
- Shugaban ofishin yan sanda na karamar hukumar Takai ne ya zama gwarzo a matakin Izu 60
Kano - Shugaban caji ofis ɗin yan sanda na karamar hukumar Takai, DPO Mahi Ahmad Ali, shine ya samu nasarar lashe musabakar karatun Alkur'ani a bangaren Izu 60.
DPO ya samu kyautuntuka kasancewa ya zo na ɗaya a Izu 60, waɗan da suka haɗa da Firji da dai sauransu.
A yau Alhamis aka kammala musabakar karatun Alkur'ani a tsakanin jami'an yan sanda, wanda hukumar yan sanda reshen jihar Kano ta shirya.
BBC Hausa ta rahoto cewa musabaƙar, wacce aka fara ranar Laraba 17 ga watan Nuwamba ta kunshi karatun Alkur'ani a matakin Izu 60, Izo 40, Izu 5 da kuma Izu 2.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Musabakar da aka shirya a hukumar ta kunshi dakarun yan sanda kuma mahaddata Alkur'ani a matakai daban-daban.
Sauran waɗan da sukasamu nasara
Kazalika rahoto ya nuna cewa mataimakin sufetan yan sanda, ASP Salihu Isamil, shi ya zamo na ɗaya a musabakar karatun Izu 40.
Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero, ya baiwa kwamishinan yan sandan jihar Kano, Sama'ila Dikko kyauta ta musamman.
Wakilin sarkin a wurin taron, Sheikh Aliyu Harazumi, shine ya mika wa kwamishina kyautar.
A cewarsa sarkin ya ba shi wannan kyautar ne saboda shine kwamishina na farko a jihar da ya shirya musabaka tsakanin jami'an yan sanda.
Hotunan bada kyauta
A wani labarin na daban kuma Hukumar Aikin Hajji ta kasa NAHCON ta tabbatar da cewa a 2022 yan Najeriya zasu samu damar yin aikin hajji
Kwamishinan labarai, tsare-tsare da bincike, Sheikh Mamoh, yace suna da tabbacin maniyya za su sauke farali a bana 2022
A wata fira da wakilin mu, kwamishinan ya yi kira ga maniyyata su fara shiri tun yanzu domin sauke farali idan Allah ya so.
Asali: Legit.ng