'Yan ajin 'Open Diaries' sun bijirewa malama kan kudin shiga ajin WhatsApp N3k
- Kirkirar aji a kafar WhatsApp ya jawo cece-kuce yayin da wata malamar gyaran aure ta bayyana bukatar a biya ta kudi a shiga aji
- Mutane da dama sun bayyana kokensu kan yadda malamar ta sauya daga yiwa mutane ajin kyauta zuwa karbe kudi a hannunsu
- Wasu kuwa sun bayyana goyon baya, yayin da malamar ta bayyana abubuwa masu muhimmanci da za a koya a ajin
Kano - Wata malamar gyaran aure a Kano ta janyo cece-kuce kan karbar Naira 3,000 a matsayin kudin rajista ga mai son shiga ajinta na WhatsApp don koyar da zamantakewar aure.
Malamar, Fatima Fouad Hashim, wacce kuma ita ce ta kafa shafin Open Diaries ta ce ajin nata an kirkirareshi ne domin ‘yan aji su rika bayyana sirrinsu, su tattauna batun dangantaka da aure, inda ta bayyana cewa N3,000 ne a yanzu kudin zaman ajin na shekara daya.
Open Diaries sanannen dandalin sada zumunta ne a Facebook wanda galibi ’yan Arewa ke baje kolin sirrinsu, ba da labaran rayuwarsu, musamman kan batutuwan dangantaka da rikicin aure don sauran 'yan aji su tattauna akai da kuma bayar da shawarwari.
Martanin 'yan aji
Jim kadan bayan yada hoton tallan shiga ajin, mutane da dama sun bayyana ra'ayoyinsu kan wannan sabon batu da basu saba gani a shafin ba.
Legit.ng Hausa ta tattaro wasu daga cikin abubuwan da aka tofa a shafin.
Smart Ajiya ya ce:
"Wallahi gari insai flavor shisha, malaman da kullum muna jinsu, wani shegenma wa'azinsa ke hanani bacci."
Kudin yayi yawa Gsky kuma fa rajistan duk shekara ne
Najeeb Muhammad Kibeeya yace:
"Duk da haka za ka sayi data, wannan rayuwa ba sauki a cikinta."
Muhammad Hauwa tace:
"Wai...3k a wannan Zamani Allah ya h*re ma masu shiga mukam en Facebook ne."
Fareeda M Abdullahi tace:
"Sister inna laifi arage kudin sbd kowani wata kikace ai ko albashi kake dauka kowani wata 3k ai kasamu nadogaro da kanka."
Auwal Umar ya yaba yunkurin, amma ya yi tambaya mai ma'ana:
"Yunkuri mai kyau kamar yadda aka ce ajin na mata zalla ne amma ta yaya za ki iya tace lambobin WhatsApp din maza da suka zabi amfani da hoton mace a madadin nasu..."
SSS sun kame matashin da ya zolayi Zainab Nasir kan auren 'yar gwagwarmaya Malala
A wani labarin, hukumar tsaron farin kaya ta SSS a Kano ta kama wani mai amfani da kafar Facebook, Ibrahim Sarki Abdullahi, da laifin zolayar wata mai fafutukar kare hakkin mata, Zainab Nasir kan auren 'yar fafatuka Malala.
Wata majiya a ofishin hukumar ta Kano ta tabbatar wa Daily Nigerian kama Mista Abdullahi, inda ta ce ana yi masa tambayoyi ne saboda taba mutuncin Zainab.
A baya dai Zainab ta bayyana ra'ayin cewa "aure ba nasara ba ne", kuma hakan ya haifar da cece-kuce a kafar Facebook, lamarin da yasa ta shahara.
Asali: Legit.ng