Labarin rigar mama ta lu'u-lu'u a kayan Diezani: Shugaban EFCC ya yi karin haske

Labarin rigar mama ta lu'u-lu'u a kayan Diezani: Shugaban EFCC ya yi karin haske

  • Shugaban hukumar EFCC, Abdulrasheed Bawa, ya musanta labarin da ake yadawa na cewa an samu rigunan mama na lu'u-lu'u daga Diezani
  • Bawa ya ce shi ke jagorantar binciken tsohuwar ministan man fetur, babu wata rigar mama ta lu'u-lu'u da suka samo yayin bincike
  • Diezani Alison Madueke ta tattara komatsanta tare da barin kasar nan tun bayan hawan mulkin Buhari kan zarginta da satar $2.5 biliyan

Abdulrasheed Bawa, shugaban hukumar yaki da rashawa tare da hana yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa, EFCC, ya ce babu wasu rigunan mama da aka samo daga Diezani Alison-Madueke, tsohuwar ministar man fetur, TheCable ta wallafa.

Diezani, wacce ta hanzarta barin kasar nan bayan tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ya mika mulki ga shugaban kasa Muhammadu Buhari a 2015, an zarge ta da sace $2.5 biliyan daga gwamnatin tarayya yayin da ta ke minista, lamarin da ta musanta.

Kara karanta wannan

Labari da Hotuna: Gini ya sake kifewa kan mutane a Jihar Legas, Jami'ai sun fara aikin ceto

Labarin rigar mama ta lu'u-lu'u a kayan Diezani: Shugaban EFCC ya yi karin haske
Labarin rigar mama ta lu'u-lu'u a kayan Diezani: Shugaban EFCC ya yi karin haske. Hoto daga thecable.ng
Asali: Twitter

Tuni hukumar EFCC ke kokarin dawo da ita kasar Najeriya,

A watan Oktoba, gwamnatin tarayya ta jero wasu kadarori da ta kwace daga Diezani wanda suka hada da tamfatsesen gida a Banana Island Foreshore Estate, Ikoyi, Lagos.

Sauran abubuwa da aka samu daga wurinta sun hada da rigunan amare 125, kananan riguna 13, rigunan matse tumbi 41, fulawoyi 73, suit 11, rigunan mama da ba a ganinsu 11, mayafai 73, rigunan mama 30, fankoki 2 da sauransu.

Sai dai, rahotannin da ke yawo a lokacin sun bayyana cewa akwai rigunan mama na lu'u-lu'u wadanda aka kwace daga wurin tsohuwar ministar.

A yayin jawabi a ranar Laraba yayin wani shiri a gidan talabijin na TVC, shugaban EFCC ya ce babu wata rigar mama ta lu'u-lu'u daga Diezani.

Kara karanta wannan

Abubuwa 17 da ya kamata ku sani a rahoton da kwamitin Endsars ya gabatar

Bawa ya kara da cewa, daya daga cikin kalubalen da hukumar ke fuskanta ta hada da halayyar 'yan Najeriya ga hukumar.

"Sau da yawa kuna zarginmu da caccakar kafafen sada zumunta, amma ina tunanin ya dace a bamu damar ji ta bakinmu. Adalci ta wuri biyu ake ji kuma a yanke shi. Babu wani abu makamancin rigar mama ta lu'u-lu'u. Kirkirar kafafen sada zumunta ne," yace.
“Da kaina zan iya fada muku saboda ni ke jagorantar binciken, Ban san da rigar mama ta lu'u-lu'u ba. Ni ya dace in fara sani saboda ni na jagoranci binciken da komai.
"Daya daga cikin abubuwan da na fadi muku cewa shi ne babbar matsalarmu. Ya dace mu canza gaskiya," yace.

ICPC: An bankado sama da ma'aikata 50 da satifiket da shekarun bogi

A wani labari na daban, hukumar yaki da rashawa mai zaman kanta, ICPC ta kama ma'aikatan ta da satifiket na bogi da shekarun bogi wanda hakan ya shafa ma'aikata masu tarin yawa, Daily Trust ta tattaro hakan.

Kara karanta wannan

Meyasa kowace matsala ta tare a yankin Arewa, Attahiru Jega ya caccaki shugbaannin Najeriya

Wannan lamarin ya shafi manyan jami'an hukumar masu yawa kuma an gano cewa hakan yasa hukumar ke kokarin daukan sassaukan mataki kan wadanda lamarin ya shafa.

A kalla ma'aikata hamsin na hukumar suka bayyana gaban kwamitin tantance satifiket kuma aka gano cewa akwai banbance-banbbance a takardun makarantarsu da kuma shekarun su.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng

Tags: