Sarkin Musulmi Ya Aike da Muhimmin Sako Ga Shugaba Buhari Game da Barazanar ASUU
- Mai alfarma sarkin musulmi, Alhaji Sa'ad Abubakar III, ya yi kira ga shugaba Buhari ya cika alkawarin da gwamnatinsa ta yi wa ASUU
- Basaraken yace a musulunci, Allah ba ya ɗaukar Alkawari ya ki cikawa, kuma yana da kyau mutum ya zama mai cika alkawari
- Kazalika yace cika wa ASUU alakwarin da gwamnati ta musu ne kaɗai zai ceci ɗalibai da sake shiga wani yajin aiki
Ibadan, Oyo - Mai Alfarma Sarkin musulmi, Alhaji Sa'ad Abubakar III, ya bukaci shugaba Buhari ya girmama yarjejeniyar da gwamnatinsa ta cimma da ASUU a shekarar 2020.
Punch ta rahoto cewa Sarkin, wanda shine shugaban jami'ar Ibadan, ya yi wannan furucin ne a jami'ar ranar Laraba.
Alhaji Sa'ad Abubakar ya nemi haka ne yayin da yake jawabi a wurin bikin yaye ɗalibai na jami'ar Ibadan karo na 73 tun bayan kafa makarantar.
Shugaba Buhari na cikin mahalarta taron, kuma ya samu wakilcin mataimakin sakataren hukumar kula da jami'o'i ta kasa (NUC).
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Sarkin musulmin ya kira yi gwamnatin tarayya ta tabbata ta yi duk me yuwuwa domin cika alkawarin dake cikin yarjejeniyar da suka cimma da lakcarori domin gujewa jefa daliban jami'o'i cikin wani yajin aiki.
Wane sako ya aike wa Buhari?
Sarki musulmi yace:
"Ina kira ga mahalarcin wannan taron (shugaba Buhari) ya taimaka ya duba bukatar ASUU, mun ji labarin kungiyar ta baiwa gwamnati wa'adi ta cika yarjejeniyarsu."
"Kun cimma matsaya tsakanin ku, to ya kamata a girmama wannan alkawurran, mutumin kirki yana cika alkawarin da ya ɗauka ga kowa. A musulunci mun san Allah ba ya ɗaukar alkawari ya ƙi cikawa."
"Idan gwamnati ta ɗaukarwa ASUU wasu alƙawurra, Dan Allah ku taimaka ku cika musu, domin haka ne kaɗai zai sa jami'o'in mu su cigaba da aiki, kuma ɗaliban mu su cigaba da karatun su."
Daga karshe Sarkin ya yi kira ga gwamnati ta kara wa jami'ar Ibadan kasafin da take tura mata domin habbaka bangaren bincike da kawo cigaba.
A wani labarin kuma Basarake ya gwangwaje diyarsa da kyautar mota bayan ta kammala digiri da daraja ta farko, hotunan motar ya bar baya da kura
Basaraken Oyo, Oba Lamidi Adeyemi III, ya nuna farin cikinsa da ni'imar da Allah ya yi wa diyarsa a karatunta, ya bata kyautar dalleliyar mota.
Diyar Sarkin, Gimbiya Zainab Adebunmi Adeyemi, ta kammala karatun digiri da sakamako mafi girma, ta samu kyautar mota. Hotunan motar da suka watsu a kafafen sada zumunta ya jawo cece-kuce daga bakin mutane.
Asali: Legit.ng