An damke mutane 15 da suka kashe babban jami'in dan sanda

An damke mutane 15 da suka kashe babban jami'in dan sanda

  • Rundunar yan sandan Legas ta kama wasu mutane 12 da ake zargi da kashe wani babban dan sanda a Legas
  • An kama wadanda ake zargin ne a mabuyarsu da ke jihar Legas da Nasarawa a cewar kakakin yan sandan Legas
  • Wadanda ake zargin sun amsa laifinsu sun yi bayanin yadda suka kashe dan sandan yayin wani samame da ya kai unguwar Ajao

Jihar Legas - 'Yan sanda a jihar Legas sun ce sun kama mutane 12 da ake zargi da hannu wurin kashe babban sufritandan yan sanda Kazeem Abonde a unguwar Ajao da ke jihar.

Jaridar Premium Times ta ruwaito cewa kakakin yan sandan jihar Legas Adekunle Ajisebutu ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar.

Kara karanta wannan

An tafi har gida an bindige Shugaban kamfanin Three Brothers Mill da matarsa a Jigawa

An kashe tsohon DPOn na Ajangbandi, Mr Abode, ne a ranar 22 ga watan Satumba yayin sumame da suka kai wasu wurare da aka hana amfani da babura a Ajao Estate.

An damke mutane 15 da suka kashe babban jami'in dan sanda
An damke mutane 15 da suka halaka babban jami'in dan sanda. Hoto: Premium Times
Asali: UGC

A cewar yan sandan, bata gari masu dimbin yawa ne suka yi kwantar bauna a kofar fita daga unguwan suka kuma far wa yan sandan da bindigu, adduna da wasu muggan makamai hakan ya yi sanadin mutuwar babban dan sandan.

Kakakin yan sanda, Mr Ajisebutu ya ce binciken da sashin SCID da ke Panti ke yi na ya yi sanadin kama mutum 12 da ake zargi da yi wa dan sandan kisar gilla.

Marigayin kuma shine shugaban sashin ayyuka na rundunar yan sandan jihar Legas kamar yadda ya zo a rahoton.

Wani sashi na sanarwar ta ce:

Kara karanta wannan

Da dumi-daumi: 'Yan bindiga sun kai hari gefen FUT Minna, sun tafka mummunan barna

"An yi nasarar kama wani Abdullahi Haruna mai shekaru 23 da wasu mutane 11 da ake zargi bayan bincike da jami'an mu suka yi na makonni hudu.
"Wadanda ake zargin sun amsa cewa sun aikata laifin hadin baki, kisa, yunkurin kisa da bannata kayayyaki, an kama su ne a mabuyarsu da ke jihohin Legas da Nasarawa inda suka labe bayan aikata mummunan abin."

Wadanda ake zargin sun amsa laifinsu

Mr Ajisebutu ya ce wadanda ake zargin sun yi bayyani dalla-dalla yadda suka kashe dan sandan tare da raunata wasu abokan aikinsa.

Yan sandan sun ce za a gurfanar da wadanda ake zargin a kotun majistare da ke Yaba a ranar 17 ga watan Nuwamba.

Kwamishinan yan sandan jihar Legasm, Hakeem Odumosu ya ce za a bi shari'ar har diddigi.

Ya roki al'umma su taimakawa rundunar da bayanai masu amfani.

'Yan sanda sun yi ram da wasu samari 2 bayan sun datse wa juna hannaye yayin kwasar dambe

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun kai harin daukar fansa, sun kashe wasu matan aure tare da kone gidaje a Taraba

A wani labarin, 'yan sanda sun yi ram da samari 2 bisa kama su dumu-dumu da laifin sare wa juna hannaye, kamar yadda jaridar Premium Times ta ruwaito.

An ruwaito yadda ‘yan sandan su ka kama Adamu Mohammed da Bukar Audu, bayan sun datse wa juna hannaye yayin wani fada da su ka tafka a Garin Alkali, karamar hukumar Dapchi da ke jihar Yobe.

Premium Times ta bayyana yadda Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, Dungus Abdulkarim, a ranar Litinin a Damaturu ya bayyana a wata takarda.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164