Hotunan Shugaba Buhari yana jagorantar zaman majalisar zartarwa a fadar Villa
- Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya jagoranci zaman majalisar zartarwa a fadar Villa da ke Abuja
- Mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo, ministoci da manyan jami'an gwamnati sun halarci zaman wanda ya gudana a dakin taro na uwargidar shugaban kasa
- An fara taron ne da misalin karfe 10:00 na safiyar Laraba, 17 ga watan Nuwamba
Abuja - Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya jagoranci zaman majalisar zartarwa a ranar Laraba, 17 ga watan Nuwamba.
An fara taron ne da misalin karfe 10:00 na safe a dakin taro na uwargidar shugaban kasa da ke fadar shugaban kasa, Abuja.
Hadimin shugaban kasa a kan kafofin watsa labarai na zamani, Buhari Sallau ya wallafa hotunan taron a shafinsa na Facebook.
Mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo, Babban sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha sun halarci taron.
Hakazalika shugaban ma’aikatan shugaban kasa, Ibrahim Gambari da babban mai ba kasa shawara kan harkar tsaro, Manjo Janar Babagana Monguno sun hallara a zaman.
Babban sakataren fadar shugaban kasa, Umar Tijani ma ya halarci zaman majalisar.
Daga cikin ministocin da suka hallara akwai Atoni Janar kuma ministan shari'a, Abubakar Malami; ministan harkokin cikin gida, Rauf Aregbesola, ministan kudi, kasafin kudi da tsare-tsare, Zainab Ahmed.
Sai ministan ayyuka da gidaje, Babatunde Fashola da kuma karamin ministan ilimi, Chukwuemeka Nwajiuba.
Shugaba Buhari ya yabi Jonathan, ya ce kamarsa daban ne a kasar nan
A wani labari na daban, Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya taya tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan murnar cika shekaru 64 da haihuwa wanda ke zuwa a ranar 17 ga Nuwamba, 2021.
Shugaban, a wata sanarwa da ya fitar ranar Talata ta hannun mai magana da yawunsa, Femi Adesina, ya taya shi murnar yi wa kasa hidima, da kuma kokarin tabbatar da zaman lafiya da ci gaban dimokuradiyya a nahiyar Afirka.
A cewar wani yankin sanarwar:
"A madadin gwamnati da 'yan Najeriya, shugaban kasa Muhammadu Buhari yana mika gaisawa da tsohon shugaban kasa, Dr Goodluck Ebele Jonathan da murnar cika shekaru 64 da haihuwa, 17 ga watan Nuwamba, 2021."
Asali: Legit.ng