2022: Kano ta ware miliyan N800 domin magance talauci da rashin aiki a tsakanin mata
- Gwamnatin jihar Kano ta ware miliyan N800 domin magance talauci da rashin aiki a tsakanin mata da matasa
- Kwamishinar harkokin mata da ci gaban jama'a, Dr Zahra’u Muhammad Umar, ce ta bayyana hakan yayin da take kare kasafin kudin ma'aikatar na 2022
- Ta kuma ce ana gyare-gyare a Cibiyar gyara hali ta Kiru tare da fadadata ta yadda za a rika horar da masu shaye-shaye maza da mata su zama masu amfani
Kano - Gwamnatin jihar Kano za ta mayar da hankali wajen horar da mata da matasa a 2022 karkashin shirinta na bayar da tallafi daga matakin farko, rahoton Daily Trust.
Kwamishinar harkokin mata da ci gaban jama'a, Dr Zahra’u Muhammad Umar, ce ta bayyana hakan yayin da take kare kasafin kudin ma'aikatar na 2022 a majalisar dokokin jihar Kano.
Zahra'u ta yi bayanin cewa kimanin naira miliyan 800 aka ware domin fara aikin daga matakin farko da nufin magance talauci da rashin aikin yi.
A cewarta wadannan abubuwa biyu (talauci da rashin aiki) sune manyan matsalolin da ke addabar ci gaban mutane, ruwayar Radio Nigeria Kaduna.
Kwamishinar ta kuma bayyana cewa gwamnatin jihar ta shirya dabaru da nufin farfado da kayayyakin cikin gida, man gyada da ake sarrafawa a gida da kuma kayan cincin da mata ke yi a yankunan karkara domin dogaro da kai.
Ta ce ana gyare-gyare a Cibiyar gyara hali ta Kiru tare da fadadata ta yadda za a rika daukar dimbin masu shaye-shayen miyagun kwayoyi maza da mata domin su zama masu amfani a cikin al’umma.
Kano Tumbin Giwa: Ganduje ya dauki masu rawar koroso 45 aikin dindindin
A wani labarin, a ranar Laraba da ta gabata, gwamnatin jihar Kano ta mika takardun daukar aikin dindindin ga masu rawar gargajiya wadanda aka fi sani da 'yan rawan koroso 45 a jihar.
Sabbin ma'aikatan rawan da aka dauka aiki an saka su a matsayin kananan ma'aikata ne wadanda za su yi aiki karkashin ma'aikatar tarihi da ofishin al'adu na jihar.
A yayin mika takardun daukar aikin a ma'aikatar, kwamishinan ma'aikatar al'adu, Ibrahim Ahmad Karaye, ya yi bayanin cewa wannan kyautatawar an yi ta ne domin karrama kananan ma'aikata masu aiki tukuru.
Asali: Legit.ng