Abu daya ya rage mu kawo karshen yan ta'adda da hare-haren yan fashi a Najeriya, Hafsan Soji

Abu daya ya rage mu kawo karshen yan ta'adda da hare-haren yan fashi a Najeriya, Hafsan Soji

  • Shugaban rundunar sojin saman kasar nan, Isiaka Amao, yace abu ɗaya sojoji ke jira su kawo karshen yan ta'adda da yan bindiga
  • A cewarsa ba da jimawa ba duk wata kungiyar yan ta'adda, Boko Haram Ko ISWAP, zata zama tarihi a Najeriya
  • Majalisar dattijai ta bukaci rundunar sojin ta ƙara ninka kokarin ta wajen tabbatar da zaman lafiya

Abuja - Hafsan rundunar sojin sama, Air Marshall Isiaka Amao, ya tabbatar wa yan majalisar dattawa cewa lokaci kaɗai ya rage ayyukan ta'addanci da yan bindiga ya zama tarihi.

Punch ta rahoto cewa Amao ya bada wannan tabbacin ne kwanaki uku kacal bayan mayakan ISWAP sun kashe Janar na sojojin ƙasa a Askira Uba, jihar Borno.

Majalisar dattijai, ta hannun kwamitin sojojin sama, sun bukaci rundunar sojin su ƙara ƙaimi a yakin da suke domin tabbatar da zaman lafiya a wuraren da lamarin ya shafa.

Kara karanta wannan

Mayakan ISWAP na sake hada kansu a wurin tafkin Chadi, Ndume ya koka

Hafsan sojin sama
Abu daya ya rage mu kawo karshen yan ta'adda da hare-haren yan fashi a Najeriya, Hafsan Soji Hoto: Nigerian Air Force HQ
Asali: Facebook

Yaushe ya bada wannan tabbacin?

Hafsan sojin saman ya yi wannan furucin ne yayin da yake kare kasafin kuɗin shekarar 2022 a gaban kwamitin majalisar dattijai ranar Talata.

Yace yan ta'adda na kowane kungiya, Boko Haram ko ISWAP, suna shan luguden wuta ta ko ina kuma ba kakkautawa, wanda hakan ke tilasta musu aje makamai.

Dailytrust ta rahoto Amao yace:

"Bisa nauyin da aka dora wa rundunar sojin sama da na ƙasa, martabar Najeriya na nan yadda aka santa kuma an kare ta daga yan ta'adda da yan bindiga, waɗan da ba da jimawa ba zasu zama tarihi."

Abinda muke yi da kasafin mu - Amao

Amao ya kara da cewa kasafin kudin da gwamnati ke ingiza wa rundunar sojin sama, tana amfani da su ne wurin cigaba da yaƙar yan ta'adda.

Kara karanta wannan

Harin Fansa: Sojojin Najeriya sun hallaka kasurgumin kwamandan yan ta'adda da wasu 37 a Askira

Hakazalika yace rundunar na amfani da kuɗaɗen wajen kara kula da walwala da jin dadin jami'an soji.

"A dai-dai wannan lokaci da muke fuskantar ƙalubale, wajibi mu sa basira da tattali wajen tafiyar da kasafin kudin da muka samu."

Ku kara kokari - Majalisar dattawa

A nasa bangaren shugaban kwamitin sanatocin, Sanata Bala Ibn Na'allah, ya bukaci sojojin su yi amfani da duk abinda suka samu wajen dawo da zaman lafiya a ƙasar nan.

Ya kuma yi kira da rundunar sojin su ninka kokarin da suke wajen hana yan ta'adda da yan bindiga sakat a cikin jeji.

A wani labarin na daban kuma Shugaba Buhari ya yi kakkausan gargaɗi kan yan bindiga bayan kashe mutum 15 a kananan hukumomin jihar Sokoto

Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari , ya gargaɗi yan bindiga kada su yi tunanin banza suke ci, ba za'a kawar da su ba.

Shugaban ya kara da cewa gwamnatinsa ba zata bari yan Najeriya su cigaba da fama da ƙalubale kala daban-daban daga yan bindigan ba.

Kara karanta wannan

Borno: Yadda samamen sojoji a sansanin ISWAP ya janyo halakar sojoji

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262