Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un: Hatsarin mota ya lakume rayuka 6 tare da jikkata 19 a jihar Bauchi

Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un: Hatsarin mota ya lakume rayuka 6 tare da jikkata 19 a jihar Bauchi

  • Wani mummunan hatsarin mota ya afku a kauyen Durum da ke hanyar Bauchi zuwa Kano
  • Hatsarin wanda ya afku a ranar Litinin, 15 ga watan Nuwamba, ya yi sanadiyar mutuwar mutane shida tare da jikkata wasu 19
  • Kwamandan hukumar kula da hana afkuwar hatsarurrukan hanya reshen jihar Bauchi, Yusuf Abdullahi, ya tabbatar da afkuwar hatsarin tsakanin wasu motocin bas biyu

Jihar Bauchi - Rahotanni sun kawo cewa rayuka shida sun salwanta sakamakon wani mummunan hatsarin mota da ya afku a Bauchi a ranar Litinin, 15 ga watan Nuwamba. Lamarin ya rutsa ne da wasu motocin haya guda biyu.

Kwamandan hukumar kula da hana afkuwar hatsarurrukan hanya reshen jihar Bauchi, Yusuf Abdullahi, ya tabbatar da afkuwar lamarin a ranar Litinin, jaridar Punch ta rahoto.

Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un: Hatsarin mota ya lakume rayuka 6 tare da jikkata 19 a jihar Bauchi
Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un: Hatsarin mota ya lakume rayuka 6 tare da jikkata 19 a jihar Bauchi Hoto: Leadeship.ng
Asali: Facebook

A cewarsa, wasu mutane 19 sun jikkata a lamarin wanda ya afku a kauyen Durum da ke hanyar Bauchi zuwa Kano.

Kara karanta wannan

Abubuwa 17 da ya kamata ku sani a rahoton da kwamitin Endsars ya gabatar

Lamarin na zuwa ne kasa da kwanaki hudu bayan wasu mutane biyar sun mutu sannan uku suka jikkata a wani mummunan hatsari da ya wakana a kauyen Gubi, hanyar babban titin Bauchi-Kano.

Abdullahi ya ce a lokacin da aka kira jami'an FRSC sai da ya kwashe su tsawon mintuna 20 kafin su isa wajen hatsarin domin aikin ceto.

Ya ce:

"Hatsarin ya afku a yammacin nan (Litinin) a kauyen Durum, hanyar titin Bauchi zuwa Kano da misalin karfe 6:42 na yamma. Hatsarin ya ritsa da wasu motocin haya biyu, dukkansu motocin bas Ford Galaxy. Wani mai suna Ibrahim Abduljalal ne ke tuka daya daga cikin motoci mai lamba JJN 712 YX.
"Har yanzu ba a iya gano sunan direban motar ta biyu da lambar rajistarta ba. Hadarin ya afku ne sakamakon dadewar tayoyin daya daga cikin motocin kuma ya shafi mutane 24 da suka hada da manyan maza, babbar mace daya da kuma yarinya daya.

Kara karanta wannan

An tafi har gida an bindige Shugaban kamfanin Three Brothers Mill da matarsa a Jigawa

"Da jami'anmu suka isa wajen bayan mintuna 20 da afkuwar hatsarin, sun gaggauta daukar mutanen da abun ya ritsa da su zuwa asibitin koyarwa na jami'ar Abubakar Tafawa Balewa, Bauchi domin kula da kuma tabbatar da halin da suke ciki.
"Da suka isa chan, wani likita ya tabbatar da mutuwar maza shida. Wadanda suka jikkata sun kasance su 19 - manya maza 17, babbar mace daya da kuma karamar yarinya daya. An ajiye gawarwakinsu a wajen ajiyar gawa na asibitin, wanda za a mika su ga yan uwansu domin binne su."

Abdullahi kuma yace an kawar da duk wasu abubuwa daga kan hanyar yayin da aka mika motocin ga sashin sufurin motoci na ofishin ‘yan sanda na GRA.

Ya kuma bukaci direbobin da su guji yin ganganci a lokacin da suke tuki tare da bin ka’idojin tuka ababen hawa.

Kano: Rayuka 5 sun salwanta, mutum 2 sun jigata a mummunan hatsarin mota

Kara karanta wannan

Sabon hari: 'Yan bindiga sun farmaki mazauna a Sokoto, sun hallaka mutane da yawa

A wani labarin kuma, mun kawo a baya cewa rayuka biyar sun salwanta, wasu biyu sun samu miyagun raunika a mummunan hatsarin da aka yi wanda ya hada da wata mota kirar Volkswagen da adaidaita sahu kan titin Kwanar Dumawa zuwa Kunya a karamar hukumar Minjibir ta jihar Kano.

Mummunan hatsarin da ya auku a ranar Talata, ya ritsa da fasinjojin da ke kan hanyarsu ta zuwa kauyukan da ke kusa da wurin, Daily Trust ta wallafa.

A yayin tabbatar da aukuwar lamarin, kwamandan hukumar kula da hadurra na yankin, Zubairu Mato, ya ce hatsarin ya auku ne sakamakon tsabar gudun ababen hawan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng