Tsadar rayuwa: Sayen kayan abinci a Kogi da Jigawa ya fi Legas tsada yayin da farashi ya karu a Oktoba
- Alkaluman hauhawar farashin kayayyaki a Najeriya ya sake raguwa a watan Oktoba zuwa mafi karanci tun karshen Disambar 2020
- Duk da raguwar hauhawar farashin kayayyaki gaba daya, NBS ta nuna cewa farashin kayan abinci a kasar na ci gaba da hauhawa
- Gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari ta sha alwashin cewa ana kokarin shawo kan tsadar kayan abinci
Hukumar Kididdiga ta kasa ta bayyana cewa farashin kayayyakin abinci a kasar ya sake tashi a watan Oktoban shekarar 2021, duk da faduwar farashin kayayyaki karo na 7 a jere zuwa kashi 15.99%.
NBS ta bayyana hakan ne a cikin sabon rahotonta na farashin kayan masarufi da ta buga a shafinta na yanar gizo a ranar Litinin, 15 ga Nuwamba, 2021.
A hakikanin gaskiya, adadin hauhawar farashin kayayyaki a Oktoba na 15.99% shine adadi mafi kankanta a cikin watanni 10 da suka gabata. Tun daga farkon shekarar 2021 (Janairu zuwa Oktoba), alkaluman hauhawar farashin kayayyaki a Najeriya ya kai kashi 17.28%.
Farashin abinci
Kamar yadda Legit.ng ke da rahoto kan farashin abinci, rahoton hukumar kididdiga ta kasa ya nuna cewa a watan Oktoba an tilastawa ‘yan Najeriya kara kasafin kudin sayen abinci idan aka kwatanta da watan Satumba na 2021.
A cewar NBS farashin abinci ya karu da 18.34% a watan Oktoban 2021 idan aka kwatanta da 17.38% a watan Oktoban 2020.
Yayin da a kowane wata, farashin abinci ya karu da 0.91% idan aka kwatanta da karuwar 1.26% da aka samu a watan Satumba na 2021.
NBS ta bayyana cewa hauhawar farashin kayan abinci ya samo asali ne daga tashin farashin abinci, irinsu; kifi, ganyen shayi da koko, madara, cukui da kwai, burodi, kayan lambu da dankali, doya, da sauran sauran nau'ukansu.
Hauhawar farashin abinci a jihohi
Rahoton NBS ya nuna cewa a cikin watan Oktoba, hauhawar farashin abinci a kowace shekara ya fi muni a jihohin Kogi (23.69%), Gombe (23.29%), da Jigawa (21.91%).
Yayin da Edo (13.16%), Rivers (14.46%), da Adamawa (15.42%) suke mafi karancin raguwar hauhawar farashin kayan abinci duk shekara.
A wata-wata kuwa, duk da haka, a watan Oktoba hauhawar farashin kayan abinci ya fi muni a Kebbi (2.29%), Yobe (2.23%), Akwa Ibom (2.16%), yayin da Kano, Kogi, Osun, da Oyo basu sami hauhawar farashin kayayyaki ba.
Gwamnatin Buhari za ta saka sabon haraji, 'Pure Water' zai koma N50 nan kusa
A wani labarin, kungiyar masu samar da ruwan sha ta Najeriya (WAPAN) ta bayyana cewa farashin ruwan ‘pure water’ na iya tashi daga N20 a yanzu zuwa N50 kan idan gwamnatin tarayya ta aiwatar da shirin haraji kan abubuwan shaye-shaye na yau da kullum.
Shugaban WAPAN na kasa, Eneri Odiri Jackson ne ya bayyana hakan a wani taron da aka gudanar a Legas. 'Yan Najeriya sun shaidi tashin farashin ruwa sau uku a cikin shekarar 2021; daga N5 zuwa N10 da kuma N20.
Kwamitin Majalisar Wakilai kan Kudi a watan Agusta 2021, ya yanke shawarar cewa za ta yi wa dokar Kudi kwaskwarima don dawo da haraji kan duk wani abin sha na yau da kullum.
Asali: Legit.ng