Gaskiya ta fito: Dalibin da ya lakadawa lakcararsa duka ya bayyana dalilin dukanta
- Matashin da ya lakadawa lakcararsa dukan kawo wuka ya bayyana gaskiyar yadda lamarin ya faru har ta kai ga duka
- Ya bayyana cewa, lakcarar ta ki taimaka masa ne bayan jin kokensa da halin da ya shiga a baya-bayan na
- Ya ce ita ta fara jifansa da kofin shayi, lamarin da ya tunzura shi har ya fara dukanta a tsakiyar makaranta kowa na gani
Ilorin, Kwara - Wani dalibin ajin karshe sashen nazarin halittu na jami’ar Ilorin, Waliyullah Salaudeen, ya bayyana dalilin da ya sa ya lakada wa wata lakcararsa, Mrs Zakariyau dukan kawo wuka.
A cewar dalibin wanda aka fi sani da Captain Walz, ya yi hakan ne sakamakon kin taimakonsa da lakcarar ta yi na wajen karkata tsarin SIWES da take duba shi akai, Daily Trust ta ruwaito.
Walz ya zanta da tawagar ‘yan jaridu a harabar Jami’ar, wadanda suka gana da shi a ofishin jami’an tsaron jami'ar bayan kama shi jim kadan bayan faruwar lamarin.
Dalibin ya yi ikirarin cewa watanni kafin faruwar lamarin a ranar Alhamis din da ta gabata, an kama shi tare da kulle shi na tsawon watanni biyu a Legas wanda hakan ya sa ya kasa zuwa yin shirin na SIWES.
Da yake bayyana halin da ya shiga, Walz ya shaida wa tawagar 'yan jarida cewa ya je Allen Avenue da ke Ikeja, Jihar Legas, domin ganawa da wani abokinsa a karon farko.
Yana jiran abokin sai yaji bukatar yin fitsari.
A cewarsa:
“Na yi fitsari a kusa da wata mota da aka faka kusa da magudanar ruwa, sai wani ma’aikacin da ke wurin ya kalubalance ni.
“Sai aka zarge ni da cewa ni barawo ne kuma ba a ba ni damar bayyana kaina ba kafin dandazon mutane su zo.
“An yi mini dukan tsiya aka mika ni ga ‘yan sanda wanda hakan ya sa aka tsare ni tsawon wata biyu.
“Bayan faruwar lamarin, sai na tuntubi Mrs Zakariyau domin na bayyana mata halin da nake ciki amma ta ce babu wani taimako da za ta min, sai dai na shiga ajin gaba wanda zai haifar da karin shekara.
“A ranar Alhamis da na shiga ofishinta, ta umarce ni da na fita.
"Na matukar fusata kuma ban san abin da ya same ni ba.
“A lokacin da nake cece-kuce da ita ne ta jefa min kofin shayi da ya raunata ni, ni kuma na fara dukanta.
“Amma ba ta yi fada dani ba, na fito da ita daga ofishinta sai ta gudu.
“Na bi ta ina ci gaba da dukanta kafin mutane su zo. Na yi kokarin guduwa amma daga baya jami’an tsaron makarantar suka kama ni."
Rahotanni a baya sun bayyana magana makamanciyar wannan kan dalilin da yasa dalibin ya lakadawa malamar duka, kamar yadda Nigeria Tribune ta ruwaito.
Wani dalibin jami'a ya lakadawa malamarsa duka kawo wuka daga neman taimako
A baya kunji cewa, dalibi dake karantar kwas din Microbiology a jami'ar Ilorin, (UniLorin) ya lakadawa lakcaransa mace dukan kawo wuka.
Daily Trust tace dalibin mai suna, Captain Walz, bai samu damar yin kwas din neman sanin makamar aiki ba (SIWES), dan haka yaje neman taimakon lakcaran.
Rahotanni sun bayyana cewa lakcaran da abin ya shafa, Mrs Zakaria, ita ce zata kula da dalibin yayin da zai yi Project a 400 level.
Asali: Legit.ng