Sabon hari: 'Yan bindiga sun farmaki mazauna a Sokoto, sun hallaka mutane da yawa

Sabon hari: 'Yan bindiga sun farmaki mazauna a Sokoto, sun hallaka mutane da yawa

  • Rahotanni da muke samu sun bayyana cewa, wasu 'yan bindiga sun kai hari wani yankin Sokoto, sun hallaka mutane 15
  • Rahoton ya ce gwamnan jihar Sokoto, Aminu Tambuwal ya tabbatar da faruwar lamarin ga manema labarai yau a Litinin
  • Jihar Sokoto na daga cikin jihohin da 'yan bindiga suka addaba a 'yan kwanakin nan, lamarin da ya kai ga mutuwar mutane da yawa

Sokoto - Akalla mutane 15 ne ‘yan bindiga suka kashe yayin wasu sabbin hare-haren da suka kai wasu kananan hukumomi biyu a jihar Sokoto, gidan talabijin na Channels ya ruwaito.

Gwamnan jihar, Aminu Tambuwal, wanda ya tabbatar da harin a ranar Litinin, ya bayyana cewa kananan hukumomin da abin ya shafa sune Goronyo da Illela.

Kara karanta wannan

Har bayan wata 7, an kasa sasanta rikicin Kwankwaso da Wali a PDP

Ya bayyana cewa an kashe mutanen yankin ne a lokacin hare-haren da suka auku tsakanin daren Lahadi zuwa safiyar Litinin.

Sabon hari: 'Yan bindiga sun farmaki mazauna a Sokoto, sun hallaka mutane da yawa
Gwamnan jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal | Hoto: dailytrust.com
Asali: Facebook

Gwamna Tambuwal ya bayyana hakan ne jim kadan kafin ya gabatar da daftarin kasafin kudin jihar na shekarar 2022 ga ‘yan majalisar dokokin jihar Sokoto.

Da yake bayar da karin haske kan lamarin, ya ce an kashe mutane 12 a Illela, yayin da wasu uku suka rasa rayukansu a Goronyo.

Gwamnan ya jajantawa iyalan mamatan sakamakon hare-haren, da kuma al’ummar da abin ya shafa baki daya.

A makon da ya gabata ne rahotanni suka bayyana yadda 'yan bindiga suka addabi wasu yankunan Sokoto, inda suka sanyawa mazauna haraji.

Premium Times ta ruwaito cewa, 'yan bindigan sun fara sanya haraji a yankin Gatawa da ke jihar ta Sokoto.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Miyagun yan bindiga sun kai wani mummunan hari Kaduna, sun kashe mutane

Tsagerun yan bindiga sun sake kai harin Tegina, sun yi awon gaba da ma'aikatan ruwa

A wani labarin, Daily Trust ta ruwaito cewa aƙalla mutum 5 yan bindiga suka sace a garin Tegina, ƙaramar hukumar Rafi, a jihar Neja.

Idan baku manta ba, a farkon wannan shekaran wasu yan bindiga suka yi awon gaba da ɗaliban makarantar Islamiyya a garin Tegina.

Wata majiya ta bayyana cewa yan bindiga sun sake kai hari garin a ƙarshen makon nan, inda suka sace ma'aikata 5 a wata ma'aikata dake garin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.