Kada ku saurari abinda PDP ke fadi, so suke kawai su bata min suna: Ali Modu Sherrif ga Gwamnonin APC
- Tsohon gwamnan jihar Borno, Ali Modu Sheriff, ya yi Alla-wadai da jawabi sirri da ya fito inda ake hira kansa
- Mambobin majalisar zartaswar jam'iyyar PDP ta bayyana cewa da so samu ne Ali Modu Sherrif yaci kujerar jam'iyyar APC
- Sherrif ya yi kira ga mambobin jam'iyyar APC suyi watsi da wannan maganganu
Abuja - Wani sabon jawabin sirri da Shugabannin Jam'iyyar Peoples Democratic Party PDP sukayi kan Ali Modu Sherrif ya bayyana kafafen ra'ayi da sada zumunta.
Tsohon gwamnan jihar Borno, Sanata Ali Modu Sherrif, ya yi kira da Gwamnonin jam'iyyar All Progressives Congress (APC) da su yi watsi da wannan jawabi saboda kawai so suke su bata masa suna.
Hakazalika yayi kira ga mambobin jam'iyyar APC suyi watsi da wannan maganganu.
A Wani jawabin sirri da ya bayyana, an ji manyan jam'iyyar PDP na cewa suna son Ali Modu Sheriff ya zama sabon shugaban jam'iyyar APC saboda babu abinda zai iya tsinanawa.
A cewarsa, idan Ali Sheriff ya zama shugaban APC, toh lallai zasu lashe zabukan 2023 a bagas.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Victor Lar, Mai magana da yawun kungiyar yakin neman zaben Senator Ali-Modu Sheriff, ya bayyana cewa wannan jawabin wasu yan bakin ciki da masu yi masa hassada ne suka sakeshi.
A cewarsa:
"Muna tabbatarwa yan Najeriya cewa Sheriff zai yi aiki da zuciya daga, ba tare da nuna banbancin addini ko kabila ba idan ya zama Shugaban jam'iyyar APC na kasa."
Sabon rikici ya sake barkewa tsakanin 'yayan jam'iyyar APC a jihar Zamfara
Sabon baraka ya auku tsakanin yan jam'iyyar All Progressives Congress (APC) a jihar Zamfara kan zaben sabbin shugabannin jam'iyya a jihar.
Legit ta samu rahoton cewa barakan ya auku ne tsakanin yan bangaren tsohon gwamnan jihar, Abdul'aziz Yari da na Sanata Kabiru Marafa.
Zaku tuna cewa a watan Febrairun shekarar nan, an hada kai tsakanin bangaren Kabiru Marafa da na AbdulAziz Yari bayan shekaru uku ana rikici.
Asali: Legit.ng