Bani da kuɗin da zan siya Sahih Bukhari da Muslim saboda an gurgunta mun kasuwanci na, Sheikh Abduljabbar

Bani da kuɗin da zan siya Sahih Bukhari da Muslim saboda an gurgunta mun kasuwanci na, Sheikh Abduljabbar

  • Sheikh Abduljabbar ya shaida wa kotu cewa ba shi da kuɗi domin tun bayan da aka tsare shi kasuwancinsa ya tsaya cak
  • Malamin ya faɗi haka ne bayan Alkalin kotu ya bukace shi ya mallaki litattafan hadithi Sahih Bukhari da Sahih Muslim
  • Daga karshe kotun ta bukaci gwamnatin jihar Kano ta siya wa Malam Abduljabbar littafin guda biyu

Kano - Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara, a ranar Alhamis, ya yi korafin cewa baki ɗaya kasuwancin sa ya gurgunce tun bayan da aka tsare shi.

Dailytrust tace Malamin ya faɗi haka ne yayin da yake martani ga umarnin alkalin kotun dake masa shari'a, Mai shari'a Abdullahi Sarki Yola.

Alkalin kotu ya bukaci Abduljabbar Kabara ya mallaki litattafan Hadithi kamar, Sahih Bukhari da kuma Sahihi Muslim domin kare kansa.

Kara karanta wannan

Kano: Gwamnati za ta saya wa Sheikh Abduljabbar littafan Sahihul Bukhari da Muslim

Malam Abduljabbar
Bani da kuɗin da zan siya Sahih Bukhari da Muslim saboda an gurgunta mun kasuwanci na, Sheikh Abduljabbar Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Sheikh Abduljabbar Kabara na gaban babban kotun musulunci dake zamanta a Kofar Kudu, Kano, kan zargin yin kalaman batanci ga Anmabi Muhammad (SAW).

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Abduljabbar yace:

"Bani da kuɗin siyan waɗan nan litattafan, domin tun bayan da aka tsare ni watannin 5 da suka shuɗe, baki ɗaya hanyoyin samun kuɗina sun tsaya cak."

Wane mataki kotu ta ɗauka kan haka?

Daga nan sai kotun ta umarci gwamnatin jihar Kano ta siya wa shehin malamin waɗan nan litattafan domin ya samu damar kare kansa idan an gabatar da shaida.

A zaman sauraron shari'ar na ranar Alhamis, Malam Abduljabbar ya yi kokarin kare kansa da wani littafi, wanda masu gabatar da ƙara suka yi ƙorafin cewa baya cikin abinda shaidu suka gabatar.

Yadda zaman ya kasance

Bugu da ƙari ɓangaren masu gabatar da ƙara sun roki kotu ta umarci shugaban ɗakin aje litattafai na jami'ar Bayero ya kawo litattafan gaban kotu.

Kara karanta wannan

Kotu ta jefa Lauya Kurkuku kan zagin Kwamishanan lamarin addinai kan lamarin Abduljabbar

Kotun ta amince da bukatar ɓangaren masu gabatar da ƙara, nan take ta bada umarnin a rubuta wasika zuwa BUK, domin kawo litattafan biyu gaban ta.

Daga nan kuma kotun ta umarci wanda ake ƙara ya nemi kudi ya siya na shi litattafan biyu ba tare da wani ya shiga ba.

Abduljabbar ya sake caccakar Lauyoyinsa

A zaman da ya gabata kafin wannan Sheikh Abduljabbar ya sake caccakar Lauyoyinsa a Kotu, ya nemi a bashi dama ya kare kansa

Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara ya sake neman a bashi dama ya kare kansa saboda ya fahimci Lauyiyinsa ba zasu iya ba.

A cewar shehin Malamin Lauyoyin na shi ba su da cikakkiyar kwarewa a ilimin addini, an yi taƙaddama a zaman kotun.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262