Da Dumi-Dumi: 'Yan daba sun kutsa majalisar jihar Plateau sun tafka mummunan ta'adi

Da Dumi-Dumi: 'Yan daba sun kutsa majalisar jihar Plateau sun tafka mummunan ta'adi

  • Wasu bata gari da ba a san ko su wanene ba sun kutsa harabar majalisar jihar Plateau sun yi barna mai yawa
  • Rahotanni sun nuna cewa yan daban sun fasa gilashi da kujeru da tebura da nau'ororin AC da wasu kayayyakin
  • Yan majalisar da suka ziyarci harabar majalisar a ranar Juma'a sun nuna takaicinsu suka nemi a koma yin zaman majalisar a tsohuwar gidan gwamnatin jihar

Jihar Plateau - A daren ranar Alhamis, 11 ga watan Nuwamba wasu yan daba sun kutsa cikin harabar majalisar dokokin jihar Plateau sun yi barna, The Nation ta ruwaito.

Barnar da aka yi ya 'yan majalisar tsagin firgita kakakin majalisa Yakubu a yayin da suka kai ziyara a safiyar ranar Juma'a domin gane wa idonsu abin da ya faru.

Kara karanta wannan

An shigar da Hafsat Barauniya kotu kan amsar kudi amma taki yin aikin

Yan majalisar, bayan ziyarar da suka kai, sun kuma yi wata zaman gaggawa inda a cewarsu sun tattauna 'wasu abubuwa masu muhimmanci game da jihar.'

Da Dumi-Dumi: 'Yan daba sun kutsa majalisar jihar Plateau sun tafka ta'adi
'Yan daba sun kutsa majalisar jihar Plateau sun tafka barna. Hoto: The Nation
Asali: UGC

Yan majalisa guda 12 karkashin jagorancin Sanda ne suka yi zaman na gaggawa.

Sanda ya jagoranci zaman majalisar na mintuna 25.

Ya lissafa abubuwan da aka tattauna sun hada da tantance shugaban hukumar zabe mai zaman kanta na jihar, PLASIEC, kamar yadda gwamna Lalong ya tura sunansa ga majalisar.

Amma, yan majalisar 12 sun bukaci a dakatar da batun tantancewar domin 'majalisar baya cikin hayyacinsa'. Sun kuma bukaci a jinkirta tattaunawa kan wasu kudirori.

A koma zaman majalisa a tsohuwar gidan gwamnati

Yan majalisar yayin zamansu sun gabatar da bukatarsu ta bakin shugaban masu rinjaye, Naanlong Daniel, na neman a koma zaman majalisar a tsohuwar gidan gwamnati da ke Rayfield don su cigaba da ayyukansu har zuwa lokacin da za a gyara majalisar.

Kara karanta wannan

Da dumi-daumi: 'Yan bindiga sun kai hari gefen FUT Minna, sun tafka mummunan barna

The Nation ta ruwaito cewa a ranar Juma'a, akwai fasassun kwallabe da kujeru da tebura a harabar majalisar. An kuma lalata na'urorin AC da wasu kayayyakin sannan an tura jami'an tsaro su saka ido a wurin.

Kwamishinan yan sandan jihar Plateau, Bartholomew Onyeka ya ce 'bai cancani ya yi magana a kan lamarin ba' a lokacin da aka tuntube shi.

Amma yan majalisar tsagin Abok Ayuba sun soki zaman da aka yi a majalisar tun kafin a fara zaman.

A sanarwar da suka fitar mai dauke da sa hannun yan tsagin, sun ce zaman ya saba umurin da aka bada na cewa a dakatar da zama a halin yanzu.

Ana neman tsigaggen kakakin majalisar Plateau ruwa a jallo

A baya, kun ji cewa rikicin da ya barke a majalisar dokokin jihar Plateau ya dau sabon salo bayan an ayyana neman tsigaggen kakakin majalisar, Abok Ayuba, ruwa a jallo.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun bi gida-gida a Katsina, sun hallaka mutane tare da kone dukiyoyi

An yi fito na fito a majalisar a ranar Litinin tsakanin magoya bayan yan majalisar biyu, dukkansu yan jam'iyyar All Progressives Congress (APC) a yayin da suke kokarin karbe iko a majalisar.

Har sai da yan sanda suka iso harabar majalisar sannan suka kwantar da tarzomar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164