Ina tare da minista Malami: Mutumin da ya jagoranci samamen gidan Odili ya magantu

Ina tare da minista Malami: Mutumin da ya jagoranci samamen gidan Odili ya magantu

  • Daya daga cikin wadanda aka kama bisa zargin kai farmaki gidan mai shari’a Mary Odili, Lawrence Ajojo ya magantu
  • Ajojo ya yi ikirari cewa shi mai ba ministan shari’a, Abubakar Malami shawara ne
  • Sai dai ya ce Malami bai ba su umurnin kai farmaki gidan Justis Odili ba
  • Tuni Atoni Janar na tarayya ya karyata ikirarin wanda ake zargin, inda yace baya cikin masu bashi shawara

Lawrence Ajojo, daya daga cikin masu laifin da aka kama kan farmakin da aka kai gidan Justis Mary Odili, ya ce shi mai bayar da shawara ne ga Atoni Janar na tarayya kuma ministan shari’a, Abubakar Malami.

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa Ajojo, wanda ya yi ikirarin cewa shi babban dan sanda ne ya fadi hakan a lokacin da aka gurfanar da shi a Abuja a ranar Alhamis, 11 ga watan Nuwamba.

Kara karanta wannan

Hotunan shugaban ɗalibai da masu tsaronsa da suka ɗauki hankula: Jami'ar FUD ta bayyana gaskiyar lamari

Ina tare da minista Malami: Mutumin da ya jagoranci samamen gidan Odili
Ina tare da minista Malami: Mutumin da ya jagoranci samamen gidan Odili Hoto: Henry Echeson
Asali: Facebook

Yan bindiga sun farmaki gidan mai shari’ar na Abuja a ranar 29 ga watan Oktoba.

Lamarin ya haifar da cece-kuce. Wasu mutane sun alakanta shi da Malami wanda ya nesanta kansa daga harin.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Da yake magana da manema labarai lokacin da aka gurfanar da shi, Ajojo ya ce Malami bai bayar da umurnin kai farmakin ba, rahoton Vanguard.

“Ni ba jami’in Rundunar yan sandan Najeriya bane amma mai bayar da shawara ne ga Atoni Janar; bai aike mu kai farmaki gidan Misis Odili ba."

Malami ya karyata ikirarin Ajojo

Sai dai kuma, Malami ya karyata ikirarin Ajojo, cewa wanda ake zargin baya cikin masu bashi shawara.

A wata sanarwa da Umar Jibrilu Gwandu, hadimin labaransa, ya saki a madadinsa, Malami ya ce hakan na iya kasancewa aikin magauta.

Gwandu ya ce:

“Da dukkan gwanaye da kwararrun jami'ai da ke bangaren Babban Atoni Janar na Tarayya kuma Ministan Shari’a, gurbatattun zukata ne kadai za su yi hasashe ko tunanin cewa mai girma Atoni Janar na Tarayya kuma Ministan Shari’a zai kaskantar da kansa wajen amfani da jami'in dan sanda na bogi domin yayi aiki a matsayin mai bashi shawara."

Kara karanta wannan

Pantami bai cancanci zama farfesa ba, In Ji Ƙungiyar ASUU

Rundunar yan sanda ta yi martani

Frank Mba, jami’in hulda da jama’a na rundunar yan sanda, ya ce bayan farmakin, Malami rubuta takardar ga yan sanda, inda ya nemi ayi bincike.

Ya ce:

“Sufeto Janar na yan sanda ya yi umurnin gudanar da bincike sosai a cikin lamarin.
“Da farko, Atoni Janar na tarayya kuma ministan shari’a ya gabatar da rubutacciyar kara zuwa ofishin IGP, inda ya nemi a yi bincike a kan lamarin, Da nufin gano wadanda ke da hannu a ciki, manufarsu da kuma wadanda suka basu umurni idan har akwai wani da ke goya masu baya.”

Ba ni da hannu a dirar mikiya da jami'an tsaro suka yi a gidan Mary Odili, Malami

A baya mun kawo cewa Antoni janar na tarayya kuma ministan shari'a, Abubakar Malami, ya ce ba hannun shi balle ofishinsa a dirar mikiyar da jami'an tsaro suka yi a gidan mai shari'a Mary Odili ta kotun koli kuma matar tsohon gwamnan jihar Ribas.

Kara karanta wannan

Da Dumi: Malamin addinin musulunci da CSP na bogi na cikin mutum 14 da aka kama kan kutse gidan Mai Shari'a Odili

Daily Trust ta ruwaito cewa, wasu jami'an tsaro wadanda har yanzu ba a gano ko su waye ba sun shiga gidan alkalin wacce mijin ta ke jerin wanda hukumar yaki da rashawa ke sanye da ido a kan a cikin kwanakin nan.

Sai dai kuma, mai magana da yawun hukumar yaki da rashawan, Wilson Uwajaren ya nisanta hukumar da hannu a cikin lamarin, Daily Trust ta wallafa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng